Dankwambo, Fayose, Wike da Aduda na kokarin jan ra'ayin Goje ya koma PDP
- Jiga-jiga jam'iyya PDP na kokarin ganin tsohon gwamnan Gombe, Danjuma Goje, ya koma PDP
- Tsaffin gwamnoni biyu, Gwamna mai ci daya, da Sanatan Abuja daya tilo sun kai masa ziyara har gida
- Wannan ya biyo bayan sulhun da uwar jam'yyar APC tayi tsakanin Gwamnan Gombe da Goje
Abuja - Yayinda ake shirin zaben 2023, tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo, ya ziyarci magabacinsa, Sanata Danjuma Goje, a gidansa dake birnin tarayya Abuja.
Dankwambo ya je gidan Goje tare da manyan jiga-jigan jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP irinsu Gwamnan jihar RIvers, Nyesom Wike, tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose; da Sanata mai wakiltan Abuja, Sanata Philip Aduda.
Ziyarar wacce akayi a sirri a unguwar Asokoro, ana kyautata zaton na kokarin jan ra'ayin Goje ya koma jam'iyyar PDP, rahoton Leadership.
Goje wanda tsohon gwamna ne kuma Ministan wuta, dan jam'iyyar PDP ne kafin ya koma APC.
A karo na uku yanzu, yana wakiltar mazabar Gombe ta tsakiya a majalisar dattawan tarayya.
Tsohon gwamnan Jihar Gombe, Danjuma Goje, ya fara siyasa a 1999, lokacin da ya rike kujerar ministan wutar lantarki karkashin mulkin shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
Ya zama gwamnan Jihar Gombe a 2003 inda ya kwashe shekaru 8 a mulki.
Har yanzu bai gama ba, ya yi gaggawar wucewa majalisar tarayya a matsayin sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya.
An samu rahotanni akan yadda kusoshi daga mazabar sa suka ki amincewa da ya yi takara a 2023.
Asali: Legit.ng