Yadda aka yi kutun-kutun, aka tunbuke Sakataren APC kafin Mala Buni ya dawo daga Dubai
- An kori John James Akpanudoedehe daga matsayinsa na sakataren rikon kwarya na jam’iyyar APC
- Shugabannin kwamitin riko da shirya zabe na CECPC su ka sa hannu a tsige Sanata Akpanudoedehe
- Tun bayan da Akpanudoedehe ya fitar da sanarwa a game da sauke Mala Buni ya samu kansa a matsala
Abuja - Takarda ta fito inda aka ga cewa an sauke Sanata John James Akpanudoedehe daga kujerar sakataren kwamitin CECPC na jam’iyyar APC na kasa.
Jaridar Premium Times ta kawo rahoto a game da sila da duk yadda aka bi, aka yi waje da John James Akpanudoedehe wanda shi ne na biyu a jam’iyyar APC.
An dauki matakin tsige sakataren ne a lokacin da ‘yan kwamitin rikon kwaryan jam’iyyar suka yi wani taro kwanakin baya a sakatariyar APC da ke birnin Abuja.
Shugaban rikon kwarya, Mai Mala Buni kadai ne bai sa hannu a wannan takardar rashin amincewa da Akpanudoedehe ba, shi ma a lokacin yana ketare.
Su wanene suka sa hannu?
Legit.ng ta fahimci cewa wadanda suka amince ayi waje da sakataren sun hada da Abubakar Sani Bello, Ken Nnamani, Abubakar Yusuf, da kuma Tahir Mamman.
Ragowar su ne Abba Ali, David Lyon, da Ismail Ahmed. Sai Akinremi Olaide, Stella Okotete da James Lulu.
Gwamna Abubakar Sani Bello wanda ya karbi shugabancin APC kafin Mala Buni ya dawo, shi ne wanda ya jagoranci sauke sakataren kwamitin na rikon kwarya.
Meyasa aka yi waje da John James Akpanudoedehe?
Ba a fadi dalilin da ya sa ‘yan kwamitin CECPC suka juyawa John Akpanudoedehe baya ba, amma rahoton ya ce yana da alaka da rikicin cikin gidan jam’iyya.
Da Duminsa: Kwamitin APC Na Riko Da Buni Ke Jagoranci Ta Sallami Sakatarenta, Ta Kada Kuri'ar Rashin Gamsuwa
Sakataren ya nuna bai goyi bayan Abubakar Sani Bello ya karbi shugabancin jam’iyyar ba. Akpanudoedehe ya fito yana cewa Buni ne shugaba har gobe.
A jawabin da ya fitar, Akpanudoedehe ya ce akwai matakan da ake bi kafin a cire jam’iyya, don haka ya yi watsi da rahoton zaman Sani Bello sabon shugaba.
Tun da sakataren ya fitar da wannan jawabi a makon jiya, ba a sake jin duriyarsa ba. Sanata Akpanudoedehe ya fahimci ya takalo rigimar da ta fi karfinsa.
Ismaeel Ahmed aka bari yana yi wa ‘yan jarida bayanin halin da jam’iyyar APC ta ke ciki a lokacin da John Akpanudoedehe ya kauracewa zuwa sakatariyar APC.
Ba a sauke Buni ba - Sakataren CECPC
An ji cewa sakataren jam'iyyar APC ya musanya sauyin shugaba, ya ce Mai Mala Buni ne yake rike da CECPC, ya ce mutane su yi watsi da labaran da su ke yawo.
Sanarwar ta fito daga bakin sakataren rikon kwarya na APC, Sanata John James Akpanudoedehe a Twitter. Bayan wannan sanarwa ne sai aka ga Bello ya shiga ofis.
Asali: Legit.ng