Za a nada Gwamna mai tsantseni a mulki, mutum 50 rak aka gayyata zuwa bikin rantsarwa

Za a nada Gwamna mai tsantseni a mulki, mutum 50 rak aka gayyata zuwa bikin rantsarwa

  • A yau Alhamis ne za a rantsar da Farfesa Charles Chukwuma Soludo a matsayin gwamnan Anambra
  • Mutane 50 kadai Farfesa Charles Chukwuma Soludo ya gayyata su halarci bikin rantsuwarsa a Awka
  • Watakila sabon gwamnan ya yi hakan ne domin gudun gwamnati ta kashe kudi masu yawa a wajen biki

Anambra - Wasu daga cikin mazauna garin Akwa, babban birnin jihar Anambra sun yi tir da yadda aka hana su halartar bikin rantsar da sabon gwamna.

Jaridar Vanguard ta ce mutane 50 kadai aka aikawa goron gayyatar rantsar da Farfesa Charles Chukwuma Soludo, abin da aka saba ganin dinbin mutane.

Wannan karo, za a rantsar da Charles Chukwuma Soludo a matsayin sabon gwamnan na Anambra ne a dakin taron SSG a gidan gwamnati a garin Awka.

Kara karanta wannan

Siyasar Kaduna: ‘Yan gaban-goshin gwamna El-Rufai da za su kawo wanda zai gaji mulki

NAN ta ce a baya an saba yin irin wannan taro a babban filin Dr Alex Ekwueme Square inda mutane da-dama su ke zuwa ganin sabon gwamnan jiharsu.

Mutane 50 za su je wajen rantsuwa

Darekta-Janar na kwamitin yakin neman zaben Farfesa Soludo a zaben 2021, C-Don Adinuba, ya bada sanarwar cewa mutane 50 kurum aka gayyata zuwa bikin.

Tsohon kwamishinan yada labaran na Anambra ya nuna daidaikun mutane za su halarci rantsuwar.

Za a nada Gwamna
Charles Soludo wajen kamfe Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Wannan mataki da aka dauka bai yi wa al’umma dadi ba. Hukumar dillacin labarai tayi hira da mutanen gari, da-dama sun nuna ba su taba ganin irin haka ba.

Jama'a su na Allah-wadai

Wani mazaunin garin, Chidiebere Igbokwe ya ce rantsar da gwamna babban biki ne da yake jawo jama’a daga ko ina, don haka ba daidai ba ne a hana su zuwa.

Kara karanta wannan

Lawan, Goje, Amaechi Da Sauran Ƴan Siyasa 4 Da Ake Damawa Da Su Tun 1999

Chidiebere Igbokwe ya ce wannan ce al’ada tun daga zamanin mulkin soja har zuwa yau a jihar.

Sunny Orji wanda Lauya ne a Awka, ya ce ba daidai ba ne Farfesa Soludo ya hana wadanda suka zabe shi zuwa wajen bikin rantsar da shi a matsayin gwamna.

Jagororin jam’iyyar APGA irinsu Shedrack Nwosu sun nuna ba su san abin da ake ciki ba. Rahoton ya ce duka-duka, ‘yan jarida hudu aka gayyata bikin.

Charles Chukwuma Soludo ya ci zabe

Ba sabon labari ba ne Farfesa Charles Chukwuma Soludo ne ya lashe zaben gwamnan jihar Anambra. Farfesan zai gaji Willie Obiano wanda ya yi shekaru takwas.

Tsohon gwamnan na CBN ya doke ‘yan takara irinsu; Andy Uba, Ifeanyi Uba da Valentine Ozigbo a zaben. Hakan na nufin APGA ce za ta cigaba da mulkar jihar Anambra.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng