Mukarrabin Osinbajo ya karyata rade-radin da ke yawo a kan mataimakin shugaban kasa

Mukarrabin Osinbajo ya karyata rade-radin da ke yawo a kan mataimakin shugaban kasa

  • Farfesa Yemi Osinbajo bai yi zama da Muhammadu Buhari a kan zancen tsayawa takara a 2023 ba
  • Wani hadimin mataimakin shugaban kasar ya musanya rade-radin da ake ji kan batun yin takara
  • Laolu Akande ya ce jita-jitar mai gidansa ya fadawa Buhari yana harin kujerarsa, surutai ne kurum

Abuja - A farkon makon nan rade-radi suka fara zagaye gari cewa maganar takarar mataimakin shugaban kasa a 2023, Yemi Osinbajo ta na kara karfi.

Legit.ng Hausa ta na cikin wadanda suka kawo rahoto cewa Farfesa Yemi Osinbajo ya zauna da Muhammadu Buhari a game da burin tsayawa takara.

Bayanan da muka samu daga The Nation sun tabbatar da cewa wannan rahoto ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan

Na kusa da Buhari ga Osinbajo da Fayemi: Tinubu ya fi karfinku a zaben 2023, ku hakura kawai

Mai taimakawa mataimakin shugaban na Najeriya wajen hulda da jama’a da watsa labarai, Laolu Akande ya ce wadannan rahotannin ba gaskiya ba ne.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, Laolu Akande ya yi watsi da wannan labari da cewa ‘jita-jita ne kurum’, ya ce kawo yanzu babu gaskiya a cikinsu.

Labarin da ya zo wa Legit.ng daga bakin Akande shi ne hasashe ne kurum wasu suke ta yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban kasa
Osinbajo da Shugaban kasa Hoto: www.thestar.ng
Asali: UGC

Osinbajo ya tsaya takara?

Tun ba yau ba, an dade ana rade-radin cewa Osinbajo zai nemi shugabancin Najeriya a karkashin APC, har yau Farfesan bai fadi hakan da bakinsa ba.

Ba wannan ne karon farko da Akande ya yi gargadi a kan irin wannan jita-jita ba, ya saba cewa a ziyarci shafin Osinbajo domin samun bayanan gaskiya.

A shafin yanar gizo na http://yemiosinbajo.ng, za a samu duk wasu bayanai a kan Farfesa Osinbajo.

Kara karanta wannan

‘Yan siyasa 6 da za su iya bayyana shirin takarar shugaban kasa nan da kwanaki masu zuwa

Ina aka yi wannan?

Wani daga cikin masu ba mataimakin shugaban Najeriyan shawara ya yi martani a kan wannan rahoto, amma bai bari ‘yan jarida sun kama sunansa ba.

Jaridar ta rahoto hadimin fadar shugaban kasa yana mai cewa kafin a yarda da rahoton, dole ayi bayanin yaushe, a ina kuma ya aka yi wannan tattaunawar.

RCCG sun kutsa siyasa

A makon da ya wuce ne aka ji cewa shugabannin cocin Redeemed Christian Church of God sun bada umarni a kafa bangarorin siyasa domin tunkarar zabe.

Ana tunanin wadannan sassa na siyasa da shugabanci da za a kafa za su taimakawa Yemi Osinbajo da sauran mabiya ko fastocin cocin da za su yi takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng