Gwamna Mai Mala Buni ya baiwa Buhari hakuri, yace a bari ya dawo kujerarsa
- Bayan kalaman El-Rufa'i, da alamun ana neman sulhu tsakanin gwamnonin APC kan rikicin jam'iyyar
- Gwamna Mai Mala wanda ke Dubai yanzu ganin Likita ya nemi afuwar shugaba Buhari bisa tuhume-tuhumen da ake masa
- Gwamnonin dake goyon bayan Buni sun ce karshen mako zasu garzaya Landan ganin Buhari
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya roki Shugaba Muhammadu Buhari ya bari ya dawo kujerarsa zuwa bayan taron gangamin APC da za'ayi nan da makonni biyu.
A bisa rahoton Thisday, Buni ya tuntubi Shugaba Buhari ya gafarta masa bisa tuhume-tuhumen da ake masa kuma a bari ya dawo kujerarsa saboda kada rikici ya barke a jam'iyyar.
Bugu da kari, wasu gwamnoni masu goyon bayan Mal Mala Buni sun roki Buhari ya bari Buni ya kammala aikinsa matsayin Shugaban APC, ya mika mulki ga sabbin shugabanni sannan ya sauka.
Sun ce dalilinsu shine gudun barkewar wani sabon rikicin kotu ana saura makonni biyu kacal zaben.
A cewarsu, hakan zai fi sauki fiye da kai juna kotu da ruguza jam'iyyar gaba daya.
Bayan haka a karshen makon nan, wasu gwamnoni da masu ruwa da tsaki na shirin zuwa ganin Buhari a Landan don tattaunawa da shi.
Daya daga cikin gwamnonin yace:
"Akwai bukatar mu ga shugaban kasa don kawo karshen wannan diraman shi yasa zamu je ganinsa karshen makon nan. Sun shirya labarai iri-iri don batawa Buni suna, kuma hakan ba gaskiya bane."
"Wasu sun je sun fadawa Shugaban kasa wasu abubuwa da suka fusata shi. Shi kuma cikin fushi ya bada umurni."
"Abinda yafi fusata shugaban kasa shine lamarin kotun, saboda sun fada masa Buni na sane, amma kuma karya ne."
"Saboda haka gwamnoni zasu je Landan ganin Buhari karshen mako wanda ya hada da Antoni Janar, Abubakar Malami; mukaddashin shugaban APCn, Bello da wasu masu ruwa da tsaki."
Shugaba Buhari ya bada umurnin cire Buni, ya so ya ha'ince mu: El-Rufai
Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ba zai taba komawa kujerar Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya bayyana hakan.
A hirar da yayi a shirin Politics Today, El-Rufa'i ya ce Buni ko ya dawo an fitittikeshi daga kujerar gaba daya har abada.
Ya ce Shugaba Buhari da gwamnonin APC 19 sun yi ittifaki kan cire Mai Mala Buni.
Asali: Legit.ng