Tsohon shugaban majalisar wakilan tarayyar da ya rika karbar albashin N15, 000 ya rasu

Tsohon shugaban majalisar wakilan tarayyar da ya rika karbar albashin N15, 000 ya rasu

  • Daya daga cikin tsofaffin ‘yan siyasar kasar nan, Hon. Benjamin Akaai Chaha ya kwanta dama a jiya
  • Benjamin Akaai Chaha ya taba rike kujerar shugaban majalisar wakilan tarayya a shekarar 1983
  • Marigayin bai wuce ‘yan makonni a kan mulki ba sai sojoji suka kifar da gwamnatin Shehu Shagari
  • A wata hira da aka yi da shi a 2013, Chaha ya ce N15, 000 ne albashinsa a lokacin da yake majalisa

Benue - Daya daga cikin iyayen siyasar Najeriya a halin yanzu, Honarabul Benjamin Chaha ya rasu a ranar Laraba, 9 ga watan Maris 2022.

Tribune ta tabbatar da labarin mutuwar Hon. Benjamin Chaha wanda ya taba rike shugaban majalisar wakilan tarayya a can shekarun baya.

Rahotanni sun ce dattijon da aka haifa a shekarar 1940 ya dade yana fama da rashin lafiya. A yammacin Laraba ne jinyar ta shi ta zo karshe.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tsohon dan wasan kwallon Najeriya ya yanki jiki ya fadi matacce a Jos

Dattijon mai shekaru 82 a Duniya ya fito ne daga Katsina Ala a garin Ukum, jihar Benuwai. Malamin makaranta ne shi kafin ya shiga siyasa.

Babban ‘dan marigayin, Alkali Steven Chaha ya shaidawa manema labarin rasuwar mahaifinsu, amma bai iya bada wani karin bayani a jiyan ba.

Majalisar wakilai
'Yan Majalisar wakilai a yau Hoto: @HouseNgr
Asali: Twitter

Yau za a ji karin bayani

Da aka tambayi Chaha game da mutuwar, sai ya bayyana cewa a same shi yau (RanarAlhamis) a ofishinsa domin ya bada cikakken karin bayani.

A yau ne ake sa ran iyalin mamacin su yi wa jama’a jawabi tare da sanin lokacin da za a birne shi.

Jaridar nan ta The Nation ta ce Benjamin Akaai Chaha ya na ta jinya dama a gidansa da ke garin Makurdi, jihar Benuwai tun a kwankin baya.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun bayyana gaskiyar abin da yasa Fulani Makiyaya suka halaka mutum 7 a Taraba

Siyasar Benjamin Akaai Chaha

Benjamin Chaha ya shiga siyasa ne a jamhuriyya ta biyu, ya zama ‘dan majalisar wakilan tarayya a karkashin jam’iyyar NPN mai mulki a lokacin.

A karshen 1983 ne Benjamin Akaai Chaha ya maye gurbin Edwin Ume-Ezeoke wanda ya yi shekaru hudu yana jagorantar majalisar wakilai.

Marigayin bai dade yana rike da majalisar tarayyar ba sai aka hambarar da gwamnatin farar hula, daga nan Muhammadu Buhari ya dare kan mulki.

Rikicin APC

A APC, an ji cewa rkicin shugabanci ya raba kan Nasir El-Rufai da Dave Umahi, an rasa tantance wanene shugaban jam’iyyar tsakanin Sani Bello da Mala Buni.

Dave Umahi yana ganin babu wani rabuwar kai a jam’iyyar APC, Mai Mala Buni ya tafi hutun ganin likita ne, don haka gwamnan Neja ya ke rike da jam’iyya

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng