Babu kan ta: Kwamishinan Ganduje, Shugabannin kananan hukumomi sun je hannun DSS
- A ranar Larabar nan ne DSS ta damke wasu shugabannin kananan hukumomi biyu na jihar Kano
- Ana zargin wasu manyan ‘yan siyasa da hannu a rikicin siyasan da ya jawo rauni da asarar rayuka
- Hukumar DSS ta na kuma binciken Kwamishinan harkar kananan hukumomi, Murtala Sule Garo
Kano – Rahotanni su na nuna cewa jami’an tsaro masu fararen kaya na DSS sun kama shugabannin kananan hukumomin Gwarzo da birnin Kano.
Daily Trust ta ce ana zargin Hon. Bashir Abdullahi Kutama da kuma Hon. Faizu Alfindiki da amfani da ‘yan bangar siyasa wajen kawo rikici a jihar Kano.
Jaridar ta ce wadanda ake zargin sun jawo tarzomar wasu magoya bayan kwamishinan kananan hukumomi da na ‘dan majalisar Rano/Kibiya/Bunkure ne.
Wani babban jami’in DSS ya shaidawa Solacebase cewa Faizu Alfindiki da Bashir Kutama suna hannunsu domin amsa tambayoyi kan zargin da ake yi masu.
Haka zalika hukumar DSS ta na neman shugaban karamar hukumar Gwale, Khalid Ishaq Diso duk a kan wannan zargi na amfani da ‘yan daba wajen kawo rikici.
Rahoton Daily Post ya tabbatar da cewa an yi ram da wani daga cikin manyan hadiman gwamna Abdullahi Umar Ganduje a binciken da jami’an DSS suke yi.
Muratala Garo sun amsa tambayoyi
Labarin da mu ke samu daga jaridar Politics Digest ta tabbatar da cewa Murtala Sule Garo yana cikin wadanda DSS ta aikawa gayyata domin ya amsa tambayoyi.
A yammacin jiya ne kuma DSS ta zauna da AbdulSalam Abdulkarim Zaura, Baffa Baba Dan’gundi da Alhassan Ado Doguwa a kan rikicin siyasan da ake samu a jihar.
Kashe-kashen siyasa
Hakan na zuwa ne bayan an hallaka wasu Bayin Allah yayin da ake rantsar da shugabannin APC. Akwai wasu da yanzu suke jinya a sakamakon samun rauni.
Rikicin siyasan da ya barke tsakanin wasu magoya baya a yankunan Garo da Burkum kwanakin baya ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla hudu a Kano.
DSS ta yi Allah-wadai da bangar siyasar da ake yi a jihar wanda suka sanadiyyar rasa rayukan jama’a. Hakan ya sa ta dauki matakin hukunta duk masu hannu.
Asali: Legit.ng