Jam'iyyar APC ta maida zazzafan martani kan tsige gwamnan Ebonyi da ya sauya sheka daga PDP

Jam'iyyar APC ta maida zazzafan martani kan tsige gwamnan Ebonyi da ya sauya sheka daga PDP

  • Jam'iyyar APC ta bayyana rashin jin daɗinta bisa abinda ta kira cin mutuncin kundin mulki a hukuncin da Kotu ta yanke
  • Shugaban APC na Ebonyi, ya ce Kotu ba ta da hurumin tsige gwamna ko mataimakinsa kan sauya sheka zuwa wata jam'iyya
  • Ya yi kira ga mutanen Ebonyi su kwantar da hankula su bi doka sau da kafa, za'a ɗaukaka ƙara

Ebonyi - Jam'iyyar APC reshen jihar Ebonyi ta yi watsi da hukuncin babbar kotun tarayya dake Abuja, wanda ta kwace kujerar gwamna Dave Umahi da mataimakinsa, Dakta Kelechi Igwe.

Mutanen biyu sun rasa kujerunsu ne biyo bayan sauya shekar da suka yi daga PDP zuwa jam'iyyar APC, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Shugaban APC a jihar Ebonyi, Chief Stanley Okoro-emegha, da yake martani, ya ce alkalin Kotun ya tafka kuskure a hukuncin da ya yanke.

Kara karanta wannan

Karin bayani: PDP ta mika sunayen masu maye gurbin gwamnan APC da mataimakinsa da aka tsige ga INEC

Gwamnan Ebonyi, David Umahi
Jam'iyyar APC ta maida zazzafan martani kan tsige gwamnan Ebonyi da ya sauya sheka daga PDP Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ya bayyana hukuncin da Kotun ta yanke matsayin karan tsaye ga kundin tsarin mulkin Najeriya da aka yi wa garambawul.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban APC ya kuma bayyana cewa akwai hukuncin babbar Kotun Abakaliki da ta Zamfara, da suka yanke cewa ba zai yuwu a kwace kujerar gwamna ko mataimaki ba kan sun sauya sheka zuwa wata jam'iyya.

Mista Okoro ya caccaki mai shari'a Ekwor Iyang bisa yiwa wasu yan siyasa aiki, wanda aka shirya don cin mutuncin gwamna Umahi da mataimakinsa domin cimma wata manufa.

Wane mataki APC zata ɗauka?

Shugaban ya yi kira ga mambobi da magoya bayan gwamna a jihar su kwantar da hankulansu, kuma su cigaba da bin doka da oda, inda ya ƙara da cewa zasu ɗaukaka kara.

Channels tv ta rahoto a kalamansa ya ce:

"A bayyane take hukuncin na tattare da son zuciya kuma ba zamu amince da shi ba. Tuni dama akwai hukuncin babbar Kotun Abakaliki da Zamfara, wanda ya nuna ba mai cire gwamna da mataimakinsa daga Ofis kan sauya sheka."

Kara karanta wannan

‘Yan siyasa 9 da za su iya asarar kujerunsu a kotu a sakamakon sauya-sheka zuwa APC

"A halin yanzun babu wani abun damuwa domin tabbas zamu ɗaukaka ƙara. Muna kiran kowane mamba da magoya baya su kwantar da hankali su bi doka."

A wani labarin kuma Jarumin Kannywood Lawan Ahmad ya fito takarar siyasa a jihar Katsina

Jarumin Kannywood , Lawan Ahmad, ya tabbatar da shiga tseren takarar mamba mai wakiltar Bakori a majalisar dokokin Katsina.

Jarumin wanda tauraruwarsa ke haskawa a shirin Izzar So da sunan Umar Hashim, ya fito siyasar ne karkashin jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262