Duk da yana Landan, Buhari ya tuna da Osinbajo yayin da ya cika shekara 65 da haihuwa
- A rana irin ta yau ne mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo yake bikin murnar kara shekara
- Shugaba Muhammadu Buhari ya aikowa mataimakinsa sakon taya shi farin cikin wannan ranar
- Ta bakin Femi Adesina, shugaban Najeriyar ya yaba da irin gudumuwar da Osinbajo yake badawa
FCT, Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya yaba da amfani, amana da kuma irin jajircewa wajen aiki na mataimakinsa watau Farfesa Yemi Osinbajo.
Shugaban Najeriyan ya bayyana hakan ne yayin da Farfesa Yemi Osinbajo ya cika shekara 65 a yau. Jaridar The Nation ta fitar da wannan rahoton dazu.
Muhammadu Buhari ya fitar da jawabi na musamman ta bakin babban hadiminsa, Femi Adesina, inda ya yabi gudumuwar Yemi Osinbajo a gwamnatinsa.
Mai girma shugaban kasar ya ce a matsayinsa na Lauya, jagora, masani kuma Fasto, Farfesa Osinbajo ya jawo gwamnatin APC ta shiga cikin al’umma.
Jawabin shugaban kasa
“A madadin majalisar zartarwa, gwamnati da mutanen Najeriya, shugaban kasa Muhammadu Buhari yana taya mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo murnar wannan lokaci na cikarsa shekara 65 a ranar 8 ga watan Maris 2022.”
“Ya shiga cikin sahun sauran jama’a, yana taya ‘yanuwa, abokai da makusanta taya shi murna.”
Osinbajo yana taka rawar gani
“Shugaba Buhari ya san gudumuwar da mataimakin shugaban kasa yake badawa a kasar nan, a matsayinsa na lauya, masani, shugaba kuma Fasto.”
“Yana aiki tukuru, ya sadaukar da kansa wajen ganin gwamnati ta rabi mutane, ta kuma kawo mutane a gwamnati ta hanyar shigo da tsare-tsaren da suke taimakon cigaban jama’a.”
“Yayin da wannan lauya kuma masani ya cika shekara 65, shugaban kasa yana mai tabbatar da amana da sadaukar da kansa, wanda abin ayi misali ne.”
“Musamman wajen kula da tattalin arziki wanda ya hada da zama da shugabannin gwamnati da ‘yan kasuwa da sauran jami’an gwamnati domin tabbatar da walwala da jin dadin ‘yan Najeriya.” - Femi Adesina.
A karshe, Channels TV ta rahoto Muhammadu Bhari yana rokon Ubangiji ya karawa mataimakinsa lafiya, basira da karfi domin ya bautawa kasarsa.
Shari'ar dokar zabe
Dazu aka ji cewa babban kotun tarayya mai zama a garin Abuja ta hana shugaba Muhammadu Buhari da wasunsa wasa da sabon dokar zabe da aka shigo da shi.
Mai shari’a Inyang Ekwo ya amince da karar da jam’iyyar PDP ta shigar, ya ce ba za a iya wasa da wannan doka ba tun da shugaban kasa ya rattaba hannunsa a kai.
Asali: Legit.ng