Bello ya zama Shugaban APC na rikon kwarya, Buhari ya yarda a tunbuke Mala Buni
- Muhammadu Buhari ya karbi shawarar wasu gwamnonin APC, ya yarda a sauke Mai Mala Buni
- Shugaban kasa ya dauki wannan mataki kafin ya bar Najeriya zuwa Landan a karshen makon jiya
- Gwamnonin sun nunawa shugaban kasa cewa Buni bai shirya gudanar da zaben shugabanni ba
- Jam'iyyar APC ta karyata wannan labari, ta ce rade-radi ne da ba su da kanshin gaskiya ko kadan
Abuja - Lissafin jam’iyyar APC ya canza yayin da ake zargin shugaban kasa Muhammadu Buhari da amincewa a sauke Mai Mala Buni daga kan mukaminsa.
Gidan talabijin na Arise TV ta kawo rahoto cewa Mai girma Muhammadu Buhari ya yi na’am da a tunbuke Mala Buni daga shugaban APC na rikon kwarya.
A daidai wannan lokaci kuma ya amince da nadin gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, a matsayin sabon shugaban jam’iyya na kasa na rikon kwarya.
Wasu gwamnonin APC ake zargin sun kai wa shugaban kasar karan Mala Buni, suka nuna masa cewa bai da shirin gudanar da zaben shugabannin jam’iyya.
Muhammadu Buhari ya karbi maganganun da wadannan gwamnoni su ka kawo, ya bada umarni ayi maza a tunbuke gwamnan Yobe, a maye gurbinsa da wani.
Mala Buni yana Dubai
Rahoton ya ce a halin yanzu, gwamnan jihar Yobe watau Mai Mala Buni yana asibiti a Dubai. Hakan ta sa bai samu damar da zai kare kan shi a Aso Villa ba.
Ministan shari’a, Abubakar Malami da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha sun yi yunkurin sa baki, su hana Buhari ya dauki wannan matakin.
Ba za a samu matsala ba?
Masu wannan ra’ayin sun nunawa shugaba Buhari cewa majalisar kolin APC na NEC ce kadai ta ke da hurumin da za tayi waje da shugaban jam’iyya na kasa.
Bugu da kari, ba za a iya tsige Mala Buni kai-tsaye ba sai an sanar da shi mako guda kafin a sauke shi. Akasin hakan ya na iya jawo jam’iyyar APC ta kare a kotu.
Idan maganar ta je kotu, hakan zai iya taba zaben shugabannin da ake sa ran ayi a karshen Maris.
Kan gwamnoni ya rabu
Wata majiya ta shaidawa This Day cewa wasu gwamnonin ba su ji dadin yadda abokan aikinsu su ka hurewa shugaban kasa kunne kafin ya wuce Landan ba.
Gwamnonin da ke tare da Mala Buni su na ganin ba gaskiya ba ne a ce bai da niyyar shirya zabe na kasa, ganin har an rantsar da kwamitocin da za su yi aikin.
Ba gaskiya ba ne - APC
Dazu nan aka ji jam'iyyar APC ta musanya wannan rahoton, ta ce har yanzu Mai Mala Buni ne shugaban CECPC, ta ce mutane su yi watsi da labaran da ke yawo.
Rashin mai da rashin wuta: Ku cigaba da juriya, ai ba mulkin Buhari aka fara rashin ba: Femi Adesina
Sanarwar ta fito daga bakin sakataren rikon kwarya na APC, Sanata John James Akpanudoedehe PhD a shafin Twitter, wanda ya ce ba haka jam'iyyarsu ta ke aiki ba.
Asali: Legit.ng