Da Dumi-Dumi: Omoyele Sawore ya bayyana shiga tseren gadon kujerar Buhari a 2023

Da Dumi-Dumi: Omoyele Sawore ya bayyana shiga tseren gadon kujerar Buhari a 2023

  • Sanannen ɗan fafutukar nan kuma mai gidan jaridar Sahara Reporters ya bayyana shiga tseren neman kujerar Buhari a 2023
  • Omoyele Sawore, ya ce ba za'a zuba ido Najeriya ta cigaba da tafiya a haka ba, dan haka zai sake shiga zaɓe kamar yadda ya yi a baya
  • A makon da ya gabata ne, Mista Sawore ya sanar da cewa zai tabbatar da kudirin takarar shugaban ƙasa a watan Maris

Abuja - Shahrarren ɗan fafutuka kuma mai gidan jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sawore, ya bayyana shirinsa na neman kujerar shugaban ƙasa a babban zaben 2023 dake tafe.

Wannan ba shine karo na farko ba, domin Sawore mamba ne a jam'iyyar African Action Congress (AAC).

Omoyele Sawore
Da Dumi-Dumi: Omoyele Sawore ya bayyana shiga tseren gadon kujerar Buhari a 2023 Hoto: Omoyele Sawore/facebook
Asali: Facebook

Haka nan kuma Sawore, shi ne ɗan takarar da ya fafata a zaben shugaban ƙasa da ya gabata a shekarar 2019 karkashin jam'iyyar AAC.

Kara karanta wannan

Allah ya yiwa mahaifiyar Sheikh Dr Bashir Aliyu Umar AlFurqan rasuwa

Ɗan fafutukar neman yancin ya bayyana shiga takarar shugaban ƙasan ne a shafinsa na dandalin sada zumunta Facebook, ranar Talata.

Da yake sanar da kudirinsa na shiga takarar kujera lamba ɗaya a Najeriya, Sawore ya sanya wani rubutu mai ɗauke da rubutun, "Ɗan takarar shugaban ƙasa, Sawore."

Ya kuma ƙara da cewa ba zai yuwu a cigaba da halin da ake ciki ba, dan haka zai tsaya takarar shugaban ƙasa a zaben mai zuwa.

Idan baku mance ba, a makon da ya gabata, Mista Sawore ya sanar da cewa zai tabbatar da shiga neman takarar shugaban ƙasa a watan Maris.

Yanzu haka ba'a kammala taron da aka shirya domin furucin ɗan fafutukan ba, kuma matasa da dama sun samu halartan wurin a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai tafi birnin Landan ganin Likita na tsawon makonni 2

A wani labarin na daban kuma An tsinci gawar mai haɗa wa Mataimakin shugaban ƙasa takalmi a daki a Abuja

Wani mazaunin yankin ya ce lokacinsa ne ya yi, domin ya kwanta lafiya lau, da safiyar Lahadi aka tsinci gawarsa a daki

Mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, wanda mamacin ya taba haɗa wa takalma, ya yi jajen rasuwarsa a wata sanarwa, tare da roko Allah ya masa rahama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262