Zamu garzaya kotu kan zaben maye gurbi na Bassa/Jos da PDP ta lashe, Dan takarar PRP
- Jam'iyyar PRP da ta zo na biyu a zaɓen maye gurbi na mazaɓar Bassa/Jos ta arewa, tace zata ɗauki matakin shari'a kan sakamakon zaben
- Dan takarar PRP, Muhammad Alkali, ya yi zargin cewa ba'a yi amfani da sakamakon wasu runfuna ba da suka zo daga baya
- Ya ce ba zasu yi shiru ba, domin sun ga abinda ya saba wa dokokin kasa da na zabe, zasu je Kotu
Jos, jihar Plateau - Ɗan takarar jam'iyyar PRP a zaben cike gurbi na mazaɓar Bassa/Jos, Muhammad Adam Alkali, yace za su kalubalanci sakamakon zaɓen da INEC ta sanar a Kotu.
VOA Hausa ta tattaro cewa bayan kammala zaɓen wanda aka gudanar ranar Asabar a kewayen mazaɓar Jos ta arewa da Bassa, hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta sanar da ɗan takarar PDP ya samu nasara.
Sai dai sakamakon zaɓen ya bar baya da ƙura, inda ɗan takarar PRP da ya zo na biyu a yawan Kuri'u ya yi zargin cewa an kulla wata makarƙashiya a wurin tattara sakamakon.
Muhammad Alkali, ya yi zargin cewa akwai sakamakon wasu runfunan zabe da aka kawo daga baya, amma aka ayyana PDP a matsayin jam'iyyar da ta samu nasara.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Haka nan kuma, ya yi ikirarin cewa akwai abubuwan da suka gani a zaɓen wanda ya saɓa wa dokar ƙasa, hukumar zabe da ma yancin ɗan Adam.
Bisa haka ne, Muhammad, ya lashi takobin cewa jam'iyyarsa ta PRP zata ƙalubalanci sakamakon a Kotu, domin nema wa al'ummar mazaɓar ƴancin su.
A kalamansa, ya ce:
"Akwai abubuwan da muka gani an yi waɗan da suka yi hannun riga da dokokin ƙasa, dokokin hukumar INEC da kuma yancin ɗan Adam, don haka zamu yi fafatukar kwato wa al'umma hakkinsu a Kotu."
Ya sakamakon zaben ya kasance?
Idan baku mance ba, a ranar Lahadi hukumar INEC ta sanar da ɗan takarar PDP, Musa Agah, a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri'u 40,343, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito
Baturen zaɓen, Oyerinde, ya ce hakan ya ba shi damar lallasa abokan takararsa na PRP wanda ya samu kuri'u 37, 754. da kuma na APC, Abbey Aku, mai kuri'u 26,111.
A wani labarin kuma Daruruwan mambobi a mahaifar dan takarar gwamna na PDP sun sauya sheka zuwa APC
Yayin da zaben 18 ga watan Yuni na gwamnan jihar Ekiti ke kara matsowa, jam'iyyar APC ta yi sabbin mambobi a Efon Alaye.
Dandazon mambobin PDP a garin da dan takarar jam'iyyar ya fito, sun sauya sheka zuwa APC mai mulkin jihar.
Asali: Legit.ng