Jam'iyyar APC ta lallasa PDP, ta lashe zaben cike gurbi a jihohi biyu

Jam'iyyar APC ta lallasa PDP, ta lashe zaben cike gurbi a jihohi biyu

  • Hukumar INEC ta sanar da sakamakon zaben maye gurbi da aka gudanar ranar Asabar a wasu mazabu na jihohin Ondo, Cross River
  • Hukumar ta sanar da yan takarar APC a mazabun guda biyu, a matsayin wadan da suka lashe zabukan da yawan kuri'u
  • Jam'iyyar APC reshen jihar Cross Ribas ta yaba wa hukumar zabe bisa shirya zabe mai tsafta da amfani da BVAS

Ondo - Hukumar zaɓe mai zan kanta ta kasa (INEC) ta ayyana Alademayokun Olarewaju na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya samu nasara a zaɓen maye gurbi a mazaɓar Akure ta arewa/Akure ta kudu, jihar Ondo.

Da yake bayyana sakamakon a Akure, baturen zaɓen, Farfesa Deji Ogunseni, yace Mista Olarewaju ya samu kuri'u 26,370 a zaɓen da aka gudanar ranar Asabar.

Yace waɗan nan kuri'u sun ba shi damar lallasa babban abokin takararsa dake biye masa Olumuyiwa Adu, na PDP da ya sami kuri'u 24,201, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Dan takarar PDP ya lashe zaben cike gurbi na Jos ta arewa

Jam'iyyar APC
Jam'iyyar APC ta lallasa PDP, ta lashe zaben cike gurbi a jihohi biyu Hoto: independent.ng
Asali: UGC

Baturen zaɓen ya kuma bayyana cewa, Olawale Oyekanmi, na AP Ya samu kuri'u 41, Oluwawemimo Fadekemi, ta ADP ta sami kuri'u 465, Joseph Ajayi, na APP ya samu kuri'u 125.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sauran sakamakon ya nuna cewa Johnson Olawusi na NRM ya samu 76, yayin da Opawole Tajudeen, na jam'iyyar SDP ya samu kuri'u 68, kamar yadda Premium Times ta rahoto

Mazaɓar Ogoja/Yala a jigar Cross Riba

Haka nan kuma, INEC ta sanar da Jude Ngaji, na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya samu nasara a zaben cike gurbi na mazaɓar tarayya Ogoja/Yala a jihar Cross Riba.

Baturen zaɓen INEC, Dakta John Edor, shine ya sanar da sakamakon zaɓen ranar Lahadi a Ogoja.

Ya ce:

"Ngaji ya samu kuri'u 22,778, waɗan da suka ba shi nasara kan abokin takararsa na kusa, Mike Usibe, na PDP wanda ya samu kuri'u 20,570"

Kara karanta wannan

Ministoci da Shugabannin Gwamnatin da ke daf da asarar kujerunsu a sabuwar dokar zabe

APC ta yaba wa INEC

Da yake tsokaci kan sakamakon zaɓen, shugaban jam'iyyar APC na jihar, Mista Alphonsus Eba, ya yaba wa hukumar INEC bisa aiki mai kyau da ta aiwatar.

"Amfani da na'urar BVAS ya taimaka sosai wajen tsaftace zaɓen har ya kasance sahihi."

Ya kuma yaba wa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, bisa rattaɓa hannu kan sabon kundin dokokin zaɓe 2022, ya zama doka.

A wani labarin kuma Jagoran APC na ƙasa Bola Tinubu ya haɗa yan Najeriya da Allah su zabe shi ya zama shugaban ƙasa na gaba a 2023

Bola Tinubu ya ce shugabancin Najeriya na bukatar mutum mai kwakwalwa kuma yana da duk abinda ake bukata.

Jagoran APC na ƙasa ya tabbatarwa yan Najeriya cewa lafiyarsa kalau, kuma basira ke mulki ba wai kafa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262