Siyasar 2023: Atiku, Tinubu da sauran ‘Yan takara za su san matsayarsu nan da kwana 92
- Dole ne kafin ranar 3 ga watan Yunin 2022 a kammala dukkanin zaben tsaida ‘dan takara a Najeriya
- Jam’iyyun siyasar kasar nan za su fito da ‘dan takararsu a zaben shugaban kasa a 2023 zuwa lokacin
- Wannan yana kunshe cikin jadawalin zaben da hukumar INEC ta kasa ta fitar a makon da ya gabata
Jaridar Daily Trust ta ce kowace jam’iyyar siyasa za ta san ‘dan takarar da zai rike mata tuta a zaben sabon shugaban Najeriyan da za ayi nan da watan Yuni.
Daga cikin wadanda ake ganin da gaske za a gwabza da su a zaben 2023 akwai jagoran APC, Bola Tinubu wanda tun tuni ya fito ya shaidawa Duniya muradinsa.
Akwai irinsu tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar wanda alamu ke nuna kwanan nan zai nemi tikitin neman takarar shugaban kasa a PDP.
Kafin ranar 3 ga watan Yunin 2022, dole jam’iyyu su tsaida wadanda za su rike masu tuta a zaben shugaban kasa. Legit.ng ta fahimci yanzu saura kwanaki 92.
A zaben shekarar badi, hukumar INEC ta bada zuwa farkon watan Yunin 2022 domin a karkare duk wata shari’a da za ta biyo bayan zaben tsaida ‘dan takara.
Haka zalika jam’iyyu su na da zuwa ranar 12 ga watan Agusta domin maye gurbin ‘yan takararsu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Abin da jam’iyyu ke cewa
Mai magana da yawun bakin shugaban APC na rikon kwarya, Mamman Mohammed ya shaidawa jaridar cewa za su fito da ‘dan takara a lokacin da aka bada.
Ita ma jam’iyyar PDP mai hamayya, ta ce za ta tsaida wadanda za su tsaya mata takara kafin ranar 3 ga watan Yuni. Debo Ologunagba ya bayyana wannan a ranar Lahadi.
Da aka tuntubi sakataren jam’iyyar NNPP na kasa, Agbo Gilbert Major ya ce sun shirya yin zaben tsaida ‘dan takara a wannan lokaci, don kuwa ba su da wani zaben.
Ra’ayin masana
Malamin ilmin siyasa a Jami’ar Bayero da ke Kano, Farfesa Kamilu Sani Fage ya ce dadin dogon jadawali shi ne jam’iyyu za su sasanta duk rikicin cikin gidansu.
Baya ga haka, al’umma su na da damar sanin ‘yan takararsu da kyau kafin a shiga babban zabe. Amma kuma yin hakan zai iya jawo hayakin siyasa ya turnuke kasa.
Shirin zaben APC
A halin yanzu da shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu ya bada wannan sanarwa, jam’iyyar APC mai mulkin kasar ta na kokarin shirya zaben shugabanninta.
Jam’iyyar APC ta sa Gwamnonin jihohin Katsina, Kogi, Imo, Ebonyi da kuma wasu manyan Ministoci masu-ci a kwamitocin da za su shirya babban zaben ta.
Akwai irinsu Farfesa Babagana Zulum, Yahaya Bello da Fani-Kayode a kwamitoci da su taimaka wajen gudanar da zaben shugabannin da za a shirya a watan Maris.
Asali: Legit.ng