Okorocha ya bada shawarar yadda za a magance rikicin APC ko APC tayi asarar Biliyoyi

Okorocha ya bada shawarar yadda za a magance rikicin APC ko APC tayi asarar Biliyoyi

  • Rochas Owelle Okorocha ya kawo shawarar da yake gani za ta magance rikicin cikin gidan APC
  • Tsohon Gwamnan na Imo ya roki a raba mukaman NWC ne a tsakanin asalin iyayen jam’iyyar APC
  • Sanata Okorocha ya ce muddin ba ayi hakan ba, kudin da su ka samu za su tafi a hayar Lauyoyi

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Owelle Okorocha ya ce za a iya shawo kan rigimar cikin gidan APC idan aka ba iyayen jam’iyya mukamai.

Daily Trust ta rahoto Rochas Owelle Okorocha yana cewa idan aka bada dama ga wadanda aka kafa APC da su su samu kujeru, rikicinsu zai zama tarihi.

Sanata Rochas Owelle Okorocha ya bayyana wannan ne a lokacin da yake zantawa da wasu manema labarai bayan an tashi zaman majalisa jiya a Abuja.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: An bayyana babban abin da zai tarwatsa jam'iyyar APC nan gaba kadan

Tsohon gwamnan yana ganin akwai bukatar a raba mukaman majalisar NWC tsakanin wadanda tun farko da su ne aka kafa jam’iyyar APC a shekarar 2013.

A cewarsa, APC ta manta da abubuwan da suka faru a baya da irin kuskuren da suka jawo jam’iyyar PDP ta rasa mulki, don haka ya ke yin kira a gyara.

Okorocha
Sanata Rochas Okorocha Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Za a kashe kudi a kotu

Sanatan na jihar Imo ta yamma yake cewa idan APC mai mulki ba ta karbi shawararsa ba, za ta kare a kotu, har ta rasa duk kudin da ta tara daga kudin saida fam.

Daily Post ta rahoto shi ne yana cewa watsi da maganarsa zai sa APC ta samu N2bn daga saida fam din takara, amma bayan nan a kashe N3bn wajen shari’a a kotu.

Kara karanta wannan

Solomon Dalung ya nemi a yafe masa na yi wa APC kamfe, ya bi Kwankwaso zuwa TMN

Da su wa aka kafa APC

“Jam’iyyun da suka kafa APC su ne – CPC da Muhammadu Buhari yake jagoranta, ACN da Asiwaju Bola Tinubu ya kawo, Abdulaziz Yari, Ali Modu Sheriff da Ogbonnaya Onu, sai Rochas Okorocha da yake jagorantar jam’iyyar APGA.”
“Dabarar da ya kamata ayi ita ce, a kira duk wadanda aka kafa jam’iyya da su, a ba su muhimman makamai, a tafi da kowa har da sababbin shiga.”
“Matsayinmu da farko shi ne a raba duk mukamai tsakanin wadannan ‘ya ‘yan tsofaffin jam’iyyu hudu da kuma ‘yan PDP da suka shigo daga baya.”

- Rochas Okorocha

Zaben APC na kasa

Dazu ku ka ji cewa akwai yiwuwar tsohon Gwamnan Nasarawa kuma Sanata mai-ci ya karbi shugabancin APC daga hannun Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni.

Alamu na nuna Sanata Abdullahi Adamu zai karbi ragamar jam’iyyar APC mai mulki bayan shugaba Muhammadu Buhari ya nuna shi ne wanda yake goyon baya.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Abin da APC ta fada sa’ilin da ASUU ta yi dogon yajin-aiki a mulkin Jonathan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng