Duk da sun kafa TMN, Kwankwaso ya na nan daram-dam-dam a jam’iyyar PDP
- Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya yi karin-haske a kan kafa tafiyar TNM
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce har zuwa yanzu shi cikakken ‘dan jam’iyyar adawa ya PDP ne
- Jagoran na tafiyar The National Movement ya ce a cikinsu akwai ‘Ya ‘yan APC, PDP har da APGA
Abuja - Rabiu Musa Kwankwaso wanda shi ne jagoran sabuwar tafiyar siyasa ta The National Movement a Najeriya, ya yi karin haske kan inda suka sa gaba.
Sanata Rabiu Kwankwaso a wata hira da ya yi da BBC Hausa, ya tabbatar da cewa bai sauya-sheka daga jam’iyya PDP kamar yadda wasu mutane ke tunani ba.
Kwankwaso ya ce The National Movement kungiya ce ba jam’iyyar siyasa ba, wanda suka kafa domin ganin an fitar da Najeriya daga halin da take ciki a yanzu.
“Ba jam’iyya ba ce, kungiya ce da muka yi ta domin tafiyar da jama’a a kan layin shugabanni na kwarai.”
“Shekara guda kenan mu na tattaunawa da mutanen da muke ganin ya dace mu tattauna da su”
“Wadannan mutane ne da kafin wannan lokaci ba su cikin Kwankwasiyya, kuma har yanzu ba lalle Kwankwasiyya suke yi ba.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Shine mu ka ga cewa ya dace a hadu, a duba abin da kasa ta ke ciki, kuma a duba abin da ya dace."
TMN ba jam’iyya ba ce
Kwankwaso ya ce a TNM akwai wanda burinsu ganin an samu zaman lafiya. Hakan ya sa suka taru a wannan tafiya da hada da 'Yan Kwankwasiyya da wasunsu.
“Yanzu duk gaba dayanmu mu na cikin jam’iyyunmu, akwai ‘Yan PDP, akwai ‘Yan APC, akwai ‘Yan APGA. Akwai wadanda ba su da jam’iyyu.”
A wata hirar wanda Ibrahim Adam, daya daga cikin matasan Jagororin Kwankwasiyya ya wallafa a Facebook, an ji Kwankwaso ya na irin wannan bayani.
APC ta gaza?
Kamar yadda bidiyon na BBC ya nuna, an ji Solomon Dalung yana cewa gwamnatin su ta APC mai-ci ba ta biya bukatar al’umma kasar kamar yadda aka so ba.
Tsohon Ministan ya ce ana fama da rashin cigaba, tabarbarewar abubuwa, kashe-kashe da durkushewar kasuwanci duk da APC ta karbi shugabanci a 2015.
Farfesa Rufai Alkali wanda shi ne Sakataren TMN ya na ganin dole a gyara halin da aka shiga ciki.
Asali: Legit.ng