Kwankwaso: Dalilin da ya sa Jonathan ya sha kashi a hannun Buhari da APC a zaben 2015
- Rabiu Musa Kwankwaso ya yi bayanin silar shan kasar Goodluck Jonathan da PDP a zaben 2015
- Madugun Kwankwasiyyar ya ce idan fuskar mutum ko turancinsa ya burge Jonathan, sai a tafi da shi
- Sanata Kwankwaso ya ce a haka Jonathan ya yi ta tara tarkace, ya dauka za su kai shi ga nasara
Abuja - Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana a game da zaben 2015, da abin da ya sa a karon farko, shugaban kasa mai-ci ya gaza lashe zaben tazarce.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wannan bayani ne a lokacin da aka yi wata hira da shi a gidan talabijin na Trust TV kwanakin baya a garin Abuja.
Legit.ng Hausa ta samu gutsuren wannan tattaunawa da aka yi da tsohon gwamnan a kafar Youtube.
Rabiu Musa Kwankwaso wanda yana cikin wadanda suka bar PDP kafin zaben 2015 ya ce tun can sun san da cewa APC za ta doke shugaba Goodluck Jonathan.
Dalili kuwa shi ne a cewar Kwankwaso, Dr. Goodluck Jonathan bai fahimci su wanene yake bukatar ya tafi da su ba, ya biyewa wasu marasa nauyi a siyasa.
Sanata Kwankwaso ya fadawa jaridar cewa a lokacin da Jonathan yake mulki, sai ya rika amfani da iya turanci ko shigar ‘yan siyasa, aka kai shi aka baro shi.
Jonathan ya biyewa wasu
“Bai san su wanene masu amfani a Kano da kasa baki daya ba. Idan fuskar mutum ko shigarsa, ko turancinsa ya burge shi, sai ya ce wannan shi ne na mu.”
“A karshe a haka shugaban kasa mai ci, ya sha kashi a zabe.” – Rabiu Musa Kwankwaso.
PDP ta na cikin matsala?
Tsohon Ministan ya ce tsohon shugaban kasar bai fahimci dawar garin ba ne, kuma bai iya wanke allonsa ba, hakan ta jawo PDP ta koma jam’iyyar adawa.
‘Dan siyasar ya bayyana cewa idan ba ayi da gaske ba, jam’iyyar PDP za ta kara maimaita irin wannan kuskure a zaben shugaban kasa da za ayi a shekarar badi.
“Haka zalika a yadda ake tafiya a yau, ban ga ta yadda PDP za ta lashe zabe ba." - Rabiu Musa Kwankwaso
Wannan bayanin duk ya biyo bayan da aka tambayi Rabiu Musa Kwankwaso ne game da matsayar tafiyar Kwankwasiyya da yake jagoranta a zaben gwamna a jihar Kano.
Sai PDP tayi da gaske
Wannan shi ne ra'ayin Sule Lamido, inda aka ji tsohon gwamnan ya na cewa ba dole ba ne mulki ya bar APC, ya koma hannun jam’iyyar PDP a zaben da za ayi a 2023.
Alhaji Lamido ya kai wa shugabannin PDP ziyara a Abuja, inda ya yi wannan jan kunnen ga jam'iyyarsa, sannan ya yi kaca-kaca da da kamun ludayin APC a yau.
Asali: Legit.ng