Takara a 2023: Atiku ya gana da gwamnoni, jagororin jam'iyyar APC, ya faɗi dalilai

Takara a 2023: Atiku ya gana da gwamnoni, jagororin jam'iyyar APC, ya faɗi dalilai

  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya musanta ganawar sirri da gwamnonin jam'iyyar APC, da jagororinta
  • Atiku, wanda ya yi karin haske ta bakin kakakinsa, Paul Ibe, yace ya je ta'aziyyar mahaifiyar Mangal a Katsina, kuma ya haɗu da jagororin APC a can
  • Duk da har yanzun bai ayyana shiga takara ba, mutane da dama na ganin ɗan asalin jihar Adamawa zai sake neman kujera lamba ɗaya a 2023

Katsina - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya musanta rahoton dake yawo cewa ya gana da wasu gwamnoni, da jagororin APC.

A wani rubutun Tuwita da Legit.ng ta gani, Paul Ibe, hadimin Atiku, ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya kai ziyarar ta'aziyya ga Alhaji Dahiru Mangal ranar 22 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari ya soke taronsa da gwamnonin APC bayan sun hallara, zai shilla turai

Atiku. Buni da Lawan
Takara a 2023: Atiku ya gana da gwamnoni, jagororin jam'iyyar APC, ya faɗi dalilai Hoto: @atiku
Asali: Twitter

A cewarsa yayin wannan ta'aziyya ta rasuwar mahaifiyar Mangal ne Atiku ya gamu da gwamnonin APC da kuma wasu ƙusoshin jam'iyyar a can.

Mista Ibe ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ba ganawa Atiku ya yi da gwamnonin APC da wasu jagororinta ba kamar yadda wasu ke yaɗa wa."
"Tsohon mataimakin shugaban ƙasa ya kai ziyara ga Alhaji Ɗahiru Mangal ranar 22 ga watan Janairu domin yi masa ta'aziyya bisa rasuwar mahaifiyarsa, kuma akai sa'a wasu gwamnoni da kusoshin APC sun je."

Shin menene ya kawo jita-jitar?

An fara yaɗa jita-jitar ne bayan Atiku ya sanya hotunansa da wasu gwamnoni da jagororin APC a shafinsa na dandalin sada zumunta Tuwita.

A hotunan dai an hangi Atiku tare da gwamna Mala Buni na jihar Yobe, gwamna Aminu Masari na Katsina da kuma shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan.

Kara karanta wannan

Zamfara: Kotu ta yi watsi da bukatar mataimakin gwamna Matawalle da jam'iyyar PDP

Bayan sanya Hotunan, Atiku ya ce:

"Da safiyar yau, na kai ziyarar ta'aziyya ga Ɗahiru Mangal a Katsina bisa rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Murja Bara'u."
"Ina addu'a Allah maɗaukakin sarki ya baiwa iyalanta hakuri, ita kuma Allah ya sa aljannar Firdausy ta zamo makomarta."

A wani labarin kuma Shugaba Buhari ya watsa wa gwamnonin APC biyu ƙasa a ido, ya ƙi amincewa da bukatarsu

Shugaba Buhari ya watsa wa wasu gwamnonin APC biyu ƙasa a Ido, ya umarci su bi matakai matukar suna son ya amince.

Rahoto ya nuna cewa gwamnonin sun garzaya ga Buhari ne domin ya goyi bayan ɗan takarar da suke so ya zama shugaban APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262