Yemi Osinbajo: Babban Fastonsa ya share masa hanyar takarar Shugaban kasa a 2023
- Yemi Osinbajo ya samu kwarin gwiwar tsayawa takarar shugabancin kasa daga Enoch Adeboye
- Jita-jita su na yawo cewa shugaban cocin RCCG, Fasto Adeboye yana tare da Osinbajo a kan 2023
- Zuwa yanzu babu wanda Farfesa Osinbajo ya fadawa cewa ya na neman kujerar shugaban kasa
Abuja - Rahoton da jaridar nan ta Daily Sun ta fitar ya na nuni ga cewa Yemi Osinbajo ya samu kwarin gwiwar neman takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Sabon rade-radin da ake ji shi ne babban limamin cocin Redeemed Christian Church of God watau RCCG, Enoch Adeboye yana tare da Mai girma Yemi Osinbajo.
Jaridar ta ce Fasto Enoch Adeboye ya duba batun takarar Osinbajo, har ya sa masa albarka. Adeboye shi ne uban gidan Adeboye a karkashin cocin RCCG.

Kara karanta wannan
2023: Dalilai 2 da suka sa Farfesa Osinbajo ba zai yi takara da Bola Tinubu ba - Jigon APC
Wata kungiyar magoya baya mai suna Omolubu2023, ta fito ta na cigaba da yi wa Farfesa yakin neman zabe, ta ce shi ne wanda ake sa ran zai ceci al’umma.
A cewar kungiyar, shugaban cocin RCCG, Fasto Adeboye yana tare da Osinbajo a kan neman mulki. Omolubu2023 ta bayyana wannan a shafin Instagram.

Source: Facebook
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rade-radin da ake samu
“A yayin da ake ta rade-radi a kan neman takararsa a yankin Kudu maso yamma, inda ya fito, Osinbajo ya yanke shawarar zai nemi shugaban kasa.”
“Bugu da kari ma, majiyoyin cikin gida su na ikirarin cewa Farfesa Osinbajo ya samu sa albarka da goyon baya a neman takararsa daga Fasto Adeboye.”
“Ka rubuta ka ajiye, zai fito takarar shugaban kasa, kuma zai bayyana nufinsa bayan zaben shugabannin APC na kasa. An kammala komai a yanzu.”
- Omolubu2023.
Ya gaskiyar abin yake?
Sai dai har yanzu babu abin da ke tabbatar da cewa mataimakin shugaban kasar zai yi takara a 2023. Asali ma sai dai akasin hakan ne za a iya tabbatarwa.

Kara karanta wannan
Yemi Osinbajo ya fadakar da jama’a a kan ‘yan siyasan da za su nesanta a zaben 2023
Mai magana da yawun Mai girma Osinbajo, Laolu Akande ya musanya jita-jitan da suke yawo a gari, ya ce mai gidansa bai kai ga daukar matsaya ba tukun.
A wani kaulin da ya fito daga bakin Daniel Bwala, Osinbajo ba zai nemi tikitin APC a zaben 2023 ba. Dalili kuwa shi ne saboda Bola Tinubu ya nuna sha'awarsa.
Daniel Bwala ya bada shawarar cewa tun da Farfesa Osinbajo ba zai yi takara ba, sai ya fadawa mabiyansa su bi bayan mai gidansa, Tinubu a jam'iyyar APC.
Asali: Legit.ng