Da Dumi-Dumi: Kotu ta yi watsi da karar dake bukatar tsige gwamnan Zamfara kan komawa APC

Da Dumi-Dumi: Kotu ta yi watsi da karar dake bukatar tsige gwamnan Zamfara kan komawa APC

  • Babbar Kotun tarayya dake Gusau, ta yi fatali da ƙarar da aka shigar gabanta kan sauya shekar gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara
  • Alkalin Kotun, Mai Shari'a Aminu Aliyu, yace Kotu ba ta da hurumin shiga lamarin siyasa da ya shafi jam'iyyu
  • A cewarsa, Kotun Zaɓe ko majalisar dokokin jiha ce kaɗai ke da hurumin tsige gwamna daga kan kujerarsa

Zamfara - Babbar Kotun tarayya dake zamanta a Gusau, jihar Zamfara ta yi fatali da ƙarar da aka shigar gabanta dake kalubalantar sauya shekar Gwamna Bello Matawalle zuwa APC.

The Cable ta rahoto cewa Matawalle, wanda ya fice daga PDP ya koma APC a watan Yuni, 2021, yace matakin da ya ɗauka zai kawo zaman lafiya a Zamfara.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnan PDP dake neman gaje Buhari ya dira Zamfara, ya gana da mataimakin Gwamna

Bashir Saleh, Ibrahim Muhammed da Andulhamid Haruna, waɗan da suƙa shigar da ƙara mai lamba FHC/GS/CS/14/2021, sun buƙaci Kotu ta umarci gwamna da mataimakinsa su fice daga Ofis.

Gwamna Bello Matawalle
Da Dumi-Dumi: Kotu ta yi watsi da karar dake bukatar tsige gwamnan Zamfara kan komawa APC Hoto: @bellomatawalle1
Asali: Twitter

Bisa rashin jin daɗin matakin gwamna na komawa APC, masu shigar da ƙarar sun roki Kotu ta bada umarnin kwace kujerun mai girma gwamna da mataimaki, Mahdi Gusau sabida a PDP suka lashe zaɓe.

Sai dai masu shigar da ƙara ta hannun Lauyansu, J. C Shaka, sun yi garambawul, tare da zare mataimakin gwamna, kasancewar bai fita daga jam'iyyar PDP ba.

Jiga-Jigan PDP sun kuma sanya hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC), jam'iyyar APC da kuma Antoni Janar na ƙasa a cikin waɗan da suke tuhuma.

Kazalika sun bukaci Kotu ta hana hukumar INEC amincewa da Bello Matawalle a matsayin gwamnan jahar Zamfara.

Kara karanta wannan

Sauya Sheka: Shugabannin majalisa biyu da wasu yan majalisun PDP uku zasu koma jam'iyyar APC

Wane hukunci Kotu ta yanke?

Da yake yanke hukunci ranar Litinin, Alkalin Kotun mai shari'a Aminu Aliyu, ya ce kotu ba ta da hurumin shiga lamarin siyasa irin wannan.

Yace kwamsutushin na PDP da kuma na mulkin Najeriya bai hana kowane mutum ya shiga jam'iyyar siyasar da ta kwanta masa a rai ba.

Premium times ta rahoto Alkalin ya ce:

"Kotun zaɓe ko kuma majalisar dokokin jiha ne kaɗai ke da hurumin tsige gwamna daga Ofishinsa."

Bayan haka Kotun ta umarci masu shigar da ƙara su biya mutanen da ake ƙara Miliyan N1m kowanen su.

A wani labarin kuma Jam'iyyar APC ta lallasa PDP da sauran jam'iyyu, ta lashe kujerun ciyamomi 21 da kansiloli 225 a jihar Kebbi

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kebbi ta sanar da sakamakon zaɓen kananan hukumomi da ya gudana ranar Asabar.

Shugaban hukumar KESIEC, Aliyu Muhammad Mera, yace jam'iyyar APC ta lashe baki ɗaya kujerun Ciyamomin jihar da Kansiloli.

Kara karanta wannan

2023: Shahararren Malamin Musulunci da Farfesoshi 8 a Kano sun tsunduma siyasa, sun zaɓi jam'iyya

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262