Jerin matsaloli 6 da Kwankwaso yake bukatar ya tsallake kafin ya shiga Aso Rock a 2023

Jerin matsaloli 6 da Kwankwaso yake bukatar ya tsallake kafin ya shiga Aso Rock a 2023

  • Alamu su na nuna cewa Rabiu Musa Kwankwaso yana harin kujerar shugaban kasa a Najeriya
  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya nemi tikitin APC a 2014 da kuma na jam’iyyar PDP a zaben 2019
  • Amma akwai wasu kalubalen da ‘dan siyasar zai iya fuskanta a hanyar cin ma wannan burin na sa

Legit.ng Hausa ta jero wasu kalubale da ake tunanin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zai iya cin karo da su a hanyar neman takara da shugabancin Najeriya.

Shakka babu, Rabiu Kwankwaso yana cikin ‘yan siyasa masu dinbin mabiya a kasar, amma duk da haka samun nasara a zaben ya wuce yawan magoya-baya.

Su menene za su iya zama masa cikas?

1. Tsarin karba-karba

Ganin Muhammadu Buhari ya fito ne daga yankin Arewa maso yamma, wasu su na da ra’ayin cewa ya kamata a mika mulki ga wani yankin dabam a 2023.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Masu son kujerar Buhari basu san dumin da ke tattara da ita ba, inji Sanusi

Matsalar farko da Rabiu Kwankwaso zai ci karo da ita a zabe mai zuwa, ita ce ya fito ne daga Kano, bangare guda da shugaban Najeriya mai-ci (Katsina).

2. Karancin kudi

Masu hasashen siyasa su na ganin cewa tsohon gwamnan na jihar Kano bai da makudan kudin da ake bukata wajen lashe zaben shugaban kasa a Najeriya a yau.

Kafin ‘dan siyasa ya iya samun tikitin tsayawa takara a jam’iyya mai kyau, har ya kai ga samun nasara a filin zabe da kotu, yana bukatar kudi masu dinbin yawa.

3. Kafuwa a jam’iyya

A 2018 ne Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sauya-sheka daga jam’iyyar APC mai mulki, ya koma PDP. Shekara hudu Kwankwaso ya yi a jam’iyyar ta APC.

Kwankwaso
Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Noble_Hassan / Twitter
Asali: Twitter

Amma har yanzu Kwankwaso bai kafu a PDP ba. Kwankwaso ya yi ta samun matsala a jihar Kano da zaben PDP na shiyya, sannan bai da kujera mai tsoka a NWC.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Na ki goyon bayan Tofa, Rimi, Buhari na zabi Abiola, Obasanjo da Jonathan

4. Amincewar manya

A cikin shekaru takwas, Injiniya Kwankwaso ya sauya-sheka sau uku. A halin yanzu ana zargin cewa kafarsa daya tana cikin PDP, daya kuma ta fita daga jam’iyyar.

Rashin samun makama ta sa manyan masu juya al’amuran siyasa ba su gama yadda da tsohon Ministan tsaron ba, wasu na zargin cewa burinsa kurum ya sa a gaba.

5. Zargin kabilanci

Ana tuhumar tsohon Sanatan na yankin Kano ta tsakiya da nuna kabilanci a tafiyar siyasarsa. Sanata Rabiu Kwankwaso ya fi farin-jini ne a jihohin Arewacin kasar nan.

Kusan zuwa yanzu, babu wasu jiga-jigan ‘yan siyasa ko manyan kudancin Najeriya da aka san su na tare da shi. Zai yi wahala ‘dan siyasa ya samu mulkin kasa a irin haka.

6. Manufofinsa

Masu zabe su na bukatar jin manufofin ‘yan takara kafin su kada masa kuri’a. Duk da Kwankwaso bai taba samun tikitin tsayawa takara ba, amma ba a gama fahimtarsa ba.

Kara karanta wannan

2023: Abubuwa 3 da za su kawowa burin Saraki tasgaro na zama Shugaban Najeriya

‘Dan siyasar bai nunawa Duniya alkiblar da zai kama idan ya samu mulki ba, ba za a iya cewa ga matsayinsa a kan tattalin arziki ba, ba a san irin kamun ludayin na sa ba.

Ba na nuna bangaranci - Kwankwaso

Kwanaki aka ji tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso ya dauko tarihin siyasa, ya bada labarin abubuwan da suka faru a zabukan 1992, 1999 da na 2011.

Rabiu Musa Kwankwaso ya wanke kansa daga zargin bangaranci, ya ce a lokacin da Jagoran su, Abubakar Rimi yake takara, shi Olusegun Obasanjo ya bi.

Haka zalika a zaben 1992, Injiniya Kwankwaso sun zabi MKO Abiola a maimakon Bashir Tofa. Abin da ya faru kenan tsakaninsa da CPC a zaben 2015.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng