2023: Dalilin da yasa wajibi yan siyasan Najeriya su yi zaman gidan gyaran Hali, Sanata Kalu
- Sanatan Abia ta Arewa, Sanata Orji Kalu, yace ya kamata baki ɗaya yan siyasan Najeriya da ma'aikata su yi zaman kaso
- Kalu, wanda yana ɗaya daga cikin yan takarar shugaban ƙasa a APC, yace zaman Kaso yana tattare da ilimi mai yawa
- A cewarsa, an zalince sa an tura shi gidan Yari, amma hakan ya zame masa Alkairi da ni'imar Ubangiji
Tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu, na ganin ya zama kusan wajibi kowane ɗan siyasa a Najeriya da ma'aikata su yi zaman gidan Kaso.
Sanata Kalu, ɗaya daga cikin yan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, kuma Sanata mai wakiltar Abia ta Arewa, ya bayyana gidan Yari a matsayin wurin koyon ilimin rayuwa.
Sanatan ya yi wannan jawabi ne ranar Jumu'a, yayin da yake fira da kafar watsa labarai ta Channels tv a cikin shirin su na, 'Siyasa A Yau.'
"Ni ba mai laifi bane, a tsaftace nake kamar komai da kuka sani," a cewar sanatan, yayin da yake martani kan tambayar da ta shafi zargin da ake masa na cin hanci.
Jigon jam'iyyar APC yace:
"Sun jefa ni gidan gyaran hali saboda haka Allah ya kaddara kuma kamata ya yi yan Najeriya su ji daɗin haka, domin na fi kirki yanzu saboda rayuwar da na yi a can."
"Ba abin da na rasa, na je gidan Gyaran hali ne domin na yi karatu, wurin wata katafariyar makarantar koyon ilimi ne. Kuma ina ganin duk wani ɗan siyasa da ma'aikaci na bukatar ya zauna a Yari, za su samu ilimin rayuwa."
Ya Sanatan ya ji da zaman gidan Yari?
A watan Disamban, 2019, wata babbar kotun tarayya dake zamanta a Legas, ta yanke wa Kalu hukuncin zaman gidan gyaran Hali na tsawon shekara 12.
Sai dai daga baya Kotun ƙoli ƙarƙashin kwamitin Alkalai 7, sun soke hukuncin da kotun baya ta yanke wa Kalu a watan Mayu, 2020.
Yayin wannan fira ta ranar Jumu'a, Sanatan ya zargi wasu manyan mutane, ciki har da tsohon shugaban ƙasa, da hannu a jefa shi cikin halin da ya shiga.
"Mafi yawan yan Najeriya sun san ban aikata laifin komai ba, shaidu 19 aka gabatar a kotu amma babu wanda ya ambaci sunana, amma wani ya biya kuɗi dan a jefa ni Yari."
"Ni abun nasara ya zama a gare ni, domin ni'ima ce Allah ya mun a rayuwa. Kamata ya yi na kasance a birnin Wuhan ranar 9 ga watan Disamba, 2019, amma an tura ni Yari ranar 5 ga watan Disamba, 2019."
A wani labarin na daban kuma Gwamnan Arewa zai fara neman shawara kan ko ya cancanta ya nemi takarar shugaban ƙasa a 2023
Gwamnan jihar Sokoto dake arewa maso yammacin Najeriya ya ce ya amince ya fara neman shawarin iyayen ƙasa kan neman takara a 2023.
Aminu Tambuwal ya nuna sha'awar neman kujera lamba ɗaya a Najeriya bayan gana wa da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP a Sokoto.
Asali: Legit.ng