Takarar 2023: Burin Tinubu, Osinbajo da Fayemi ya raba kan Gwamnonin Yarbawa a APC

Takarar 2023: Burin Tinubu, Osinbajo da Fayemi ya raba kan Gwamnonin Yarbawa a APC

  • Hankalin Gwamnonin jam’iyyar APC a kudu maso yammacin Najeriya ya rabu a kan zaben 2023
  • Akwai gwamnoni akalla uku da ake kyautata zaton su na goyon bayan takarar Bola Tinubu
  • Gwamnan jihar Ekiti ba ya tare da Tinubu ko Osinbajo, akwai alamun shi ma yana harin yin takara

Lagos – Gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyyar APC sun samu kansu a rabuwar kai a dalilin burin wasu jiga-jigan jam’iyya na neman shugaban kasa.

Wani rahoto da Vanguard ta fitar a ranar Laraba, 2 ga watan Fubrairu 2022 ya bayyana cewa Bola Tinubu, Yemi Osinbajo da Kayode Fayemi sun raba kan APC.

Yayin da har yanzu Yemi Osinbajo da Kayode Fayemi ba su bayyana matsayarsu kan neman takarar shugaban kasa ba, Bola Tinubu ya fadawa Duniya burinsa.

Kara karanta wannan

Tinubu, Saraki, Okorocha da ‘yan takaran Shugaban kasa 6 da EFCC da ICPC suke bincike

Hakan ya raba kan gwamnonin kasar Yarbawa inda aka samu gwamnonin jihohi uku da suke goyon bayan Tinubu ya nemi takara a karkashin jam’iyyar APC.

Dr. Fayemi wanda yanzu haka gwamna ne bai tare da Tinubu ko Osinbajo, ana zargin cewa shi ma yana tunanin ya fito neman tikitin APC na takara a zaben 2023.

Gwamnonin Yarbawa a APC
APC ta na kamfe a Legas Hoto: Sanwo Olu
Asali: Twitter

An raba hankalin gwamnoni

An fahimci cewa gwamnonin Legas, Osun da Ogun; Babajide Sanwo-Olu, Gboyega Oyetola da kuma Dapo Abiodun su na tare da maigidansu, Asiwaju Tinubu.

Rahotonnni sun ce shi kuma gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ya rasa wanda zai marawa baya.

Wani ya shaidawa manema labarai cewa gwamnan Ogun yana tare da Tinubu. Bangaren Tinubu ne suka yi kokarin ganin Dapo Abiodun ya zama gwamna a 2019.

Kara karanta wannan

2023: Jerin abubuwa 6 da za su tare hanyar Atiku Abubakar ya zama Shugaban Najeriya

Shi kuwa Kayode Fayemi ya na ta tuntubar mutane a game da burinsa na neman shugabanci. Shugaban na NGF yana tunanin sauran gwamnoni na tare da shi.

A jihar Osun, kotu tayi watsi da karar da bangaren Rauf Aregbesola suka shigar a kan zaben APC, hakan ya kara tabbatar da jam’iyya a hannun Gboyega Oyetola.

Gwamna daya PDP ta ke da shi a kudu maso yamma, kuma shi ne Seyi Makinde na jihar Oyo. Gwamnan ba ya goyon a sake mika mulkin Najeriya ga wani tsoho.

Rigingimun APC

Hakan na zuwa ne a lokacin da APC ta ke fama da rikicin gida a reshen jihar Ekiti a dalilin zaben fitar da gwani domin tsaida wanda zai yi takarar gwamna a 2022.

Tsohon Sakataren gwamnatin jihar Ekiti, Biodun Oyebanji, ya yi galaba a zaben fitar da gwanin da jam'iyyar APC ta shirya, wanda hakan ya bar baya da kura a jihar.

Kara karanta wannan

Tinubu ya lula kasar waje ganin Likita da hutawa bayan yawon ziyarce-ziyarcen da yayi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng