Shugaba Buhari ya aikawa Majalisa sunayen sababbin mukaman da ya nada a Gwamnati
- A yau aka ji Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wasu nade-nade a gwamnatin tarayya
- Fadar shugaban kasa ta aikawa Majalisa takarda ta na neman a rantsar da kwamishinoni a NERC
- Haka zalika, za a nada Darekta a Nigerian Midstrea & Downstream Petroleum Regulatory Authority
FCT, Abuja - Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rubutawa majalisar dattawa takarda a kan nadin mukaman da ya yi a hukumar NERC ta kasa.
Jaridar Punch ta fitar da rahoto a ranar Laraba, 2 ga watan Fubrairu 2022 cewa Mai girma Muhammadu Buhari ya nada kwamishinoni hudu a NERC.
Baya ga kwamishinonin da aka nada a hukumar NERC, shugaban Najeriyan ya zabi wanda zai zama darektan Nigerian Deposit Insurance Corporation.
Takardar shugaban kasar ta sanar da majalisar dattawan game da nadin darektan Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority.
Hukumar NERC ce ta ke kula da harkokin wutar lantarki, NDIC kuma ta na kula da bankuna. Dayan hukumar ta na sa ido a kan sha’anin man fetur na kasa.
An karanto wasikar Buhari
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya karanto wasiku ukun da suka fito daga fadar shugaban kasa a zaman da aka yi na ranar Laraba.
Dr. Yusuf Ali (Arewa maso tsakiya), Injiniya Chidi Ike (South-East), Mr. Nathan Shetty (Arewa maso gabas), su ne kwamishinonin da za su rike hukumar NERC.
Mr. Dafe Apeneye shi ne kwamishinan da aka zaba daga yankin Kudu maso kudu. Idan an tantance su a majalisar dattawa ne za su shiga ofis, su fara aiki.
Nigerian Midstream & Downstream Petroleum Regulatory Authority
Darektocin da za a tantance su rike hukumar man su ne Francis Alabi Ogali; Dr. Mustapha Lawade; Monsuru Kulia; Bashiru Sadiq, da kuma Dr. Zainab Gobir.
Newsngr ta ce a wata takarda dabam, akwai sunan Emili Chidinma Osuji da shugaba Buhari yake so a tabbatar a matsayin sabuwar shugabar hukumar nan ta NDIC.
Wadanda su ka fita zakka
Kun ji cewa mutane kan yi rububin mukami a gwamnati, musamman idan ya fito daga wajen Mai girma shugaban kasa, amma ban da irinsu Naja'atu Muhammad.
A nan mun kawo jerin mutum 5 da suka ki karbar kujerun da Shugaban kasa Buhari ya ba su.
Asali: Legit.ng