Mutum 5 da suka ki karbar kujerun da Shugaban kasa Buhari ya ba su a Gwamnatinsa

Mutum 5 da suka ki karbar kujerun da Shugaban kasa Buhari ya ba su a Gwamnatinsa

  • Mutane kan yi rububin mukami a gwamnati, musamman idan ya fito daga wajen Mai girma shugaban kasa
  • Farfesa Auwal Yadudu da makamantansa sun sha bam-bam da sauran mutane wajen kwadayin matsayi
  • Akwai wasu daidaikun mutane da shugaban Najeriyan ya ba mukami, amma su ka ce sam ba su da bukata

A wannan rahoto na musamman, Legit.ng Hausa ta bi wadanda suka ki karbar mukaman da gwamnatin Muhammadu Buhari ta ba su, da dalilan da suka bada.

1. Naja’atu Muhammad

Shahararriyar ‘yar gwagwarmayar nan, Hajiya Naja’atu Muhammad ita ce farko a jerin mu na wadanda suka ki karbar mukamin gwamnatin tarayya da Buhari ya ba ta.

An nemi Naja’atu Muhammad ta zama shugaban majalisar da ke sa ido a kan harkar jami’ar tarayya da ke Dutse, amma ta ki karbar aikin saboda ba a tuntube ta ba.

Kara karanta wannan

Kisan gilla: Bayan kisan Hanifa, wani Malami ya kashe Almajirinsa a jihar Kano

Yadda aka sanar da kujerar da aka ba ta a gidan yada labarai, haka ta fito tayi watsi da tayin.

2. Auwal Yadudu

Farfesa Auwal Yadudu yana cikin wadanda Muhammadu Buhari ya nada a matsayin sababbin shugabannin jami’o’in tarayyar nan 12 da Goodluck Jonathan ya kafa.

Auwal Yadudu a matsayinsa na kwararren masanin shari’a ya ki karbar aikin shugaban jami’ar Birnin Kebbi, dalilinsa kuwa, ba a bi ka’ida wajen nadin mukaman ba.

Shugaban kasa Buhari
Naja'atu Muhammad Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

3. Olorunnimbe Mamora

A lokacin da Muhammadu Buhari ya zabi Sanata Olorunnimbe Mamora ya zama shugaban cibiyar nan ta Abuja Investment and Infrastructure Centre, bai karbi aikin ba.

Rahotanni sun ce Mamora ya ki karbar mukamin ne saboda cire sunansa daga wadanda za a ba kujeru masu tsoka. Bayan zaben 2019 aka nada shi Minista, kuma ya karba.

Kara karanta wannan

Ganduje ya gwangwaje jarumi Naburaska da mukami a gwamnatinsa

4. Pauline Tallen

Tsohuwar mataimakiyar gwamnan jihar Filato, Pauline Tallen ba ta gamsu da kujerar Jakada da aka ba ta ba. Ita ma Tallen ta koka cewa gwamnati ba ta nemi jin ta bakinta ba.

A wancan lokaci, Hon. Tallen ta bada uzurin cewa ta na jinyar mai gidanta a Najeriya, sannan ta fito ne daga kudancin jihar Filato, amma ita ma ta karbi Minista daga baya.

5. Usman Bugaje

Shi ma Dr. Usman Bugaje bai karbi mukamin Jakada da gwamnatin Muhammadu Buhari ta ba shi ba. Wasu na ganin kujerar za ta nakasa burin siyasar da yake da ita a gida.

Tsohon ‘dan majalisar ya dade ya na neman gwamna a Katsina, kuma ya na cikin masu sukar APC. A cewarsa ayyukan da yake yi a gida ba za su bar shi ya tafi kasar waje ba.

Zawarcin gwamnan Akwa Ibom

A kwanakin baya an ji yadda shugaban majalisa, Ahmad Lawan ya ga aiki wajen Gwamnan Akwa Ibom, Udom Emmanuel ya fara zuga shi ya shigo jirginsu na APC.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari ta zabi tsohon Gwamnan Borno, ta ba shi babbar kujera a makarantar da ta gina

Sanata Ahmad Lawan ya kira gwamnan ne a lokacin da ya ziyarci garin Uyo domin bude wani aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng