Magaji na zai samu daidaitacciyar damokaradiyya da ingantaccen tsarin tsaro, Buhari
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa mulkinsa zai bar daidaitacciyar damokaradiyya da ingantaccen tsarin tsaro
- Shugaban kasan ya sanar da shugabannin kasuwanci, siyasa, kafafen sada zumunta da na kungiyoyi masu zaman kansu hakan a Abuja
- Buhari ya yi kira ga 'yan siyasa da su daina duban kujerun su, su kalli sauyin da za su iya kawowa ga al'umma yayin da suke mulki
Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara tabbatar wa da 'yan Najeriya cewa mulkinsa zai tabbatar da daidaitacciyar damokaradiyya da kuma tsarin tsaro mai kyau kafin cikar wa'adin mulkinsa a shekara mai zuwa.
Shugaban kasar ya sanar da hakan ne a wata liyafar cin abincin dare inda ya karrama kwamitin shugabannin kasuwanci, siyasa, kafafen sada zumunta da kuma shugabannin kungiyoyi masu zaman kansu a fadarsa ta Abuja.
Buhari ba zai iya tafiyar mota babu shiri ba, Fadar shugaban kasa ta yi wa PDP martani kan ziyarar Zamfara
The Nation ta ruwaito cewa, ya sha alwashin mika wa magajinsa tattalin arziki mai karfi, saisaitacce idan ya kammala mulkinsa.
The Nation ta ruwaito cewa, Shugaban kasar ya ce ya na hango kammala wa'adin mulkinsa a shekara mai zuwa kuma zai bar tarihi kan hadin kai, zaman lafiya da yalwatacciyar damakoradiyya.
Ya tabbatar wa da 'yan Najeriya cewa zai kammala lokacin karshe na wa'adin mulkinsa inda ya ke cewa:
"A hankali ina shiga shekarar karshe na a ofis. Wannan lokaci ne da na yi niyyar kare shi ba ta hanyar hada kan 'yan Najeriya, tabbatar da zaman lafiya da kuma yalwar arziki.
"Na dauko wannan hanyar kuma ina fatan za ku bani hadin kai da goyon baya ga mulki na domin cimma abinda muka yi niyya."
Ya kara da cewa:
"Ga wadanda 'yan siyasa ne, dole ne ku yi duba sama da karbar mulki kadai zuwa yadda za ku yi amfani da mukaman wurin kawo sauyi a al'umma. Ga 'yan kasuwa maza da mata daga cikin ku, akwai daukaka sosai wurin bautawa jama'a."
Buhari ba zai iya tafiyar mota babu shiri ba, Fadar shugaban kasa ta yi wa PDP martani kan ziyarar Zamfara
A wani labari na daban, fadar shugaban kasa tace tsokacin da jam'iyyar PDP tayi game da fasa kai ziyara Zamfara da shugaba Muhammadu Buhari yayi alamar neman rigima ne da tsegumi.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shirya kai wa Zamfara ziyara a ranar 27 na watan Janairu don tattaunawa game da matsalar rashin tsaro a jihar sannan ya jajanta wa mutane a kan hare-haren da aka kai kwanan nan a karamar hukumar Anka da Bukkuyum.
Sai dai, yayin da aka fara shirye-shiryen tarbar sa, Bello Matawalle, gwamnan Zamfara, ya bayyana cewa shugaban kasar zai canza lokacin ziyarar don matsalar rashin ganin da jirgi ke fama da shi saboda buji.
Asali: Legit.ng