Yanzu-Yanzu: Gwamnan PDP a Arewa ya bayyana kudurinsa na gaje kujerar Buhari a 2023
- Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana shiga tseren zama shugaban ƙasa a zaɓen 2023 dake tafe
- Tambuwal ya ce a shirye yake ya kawo ƙarshen baki ɗaya matsalolin Najeriya idan ya zama shugaban ƙasa
- Gwamnan ya shiga jerin masu bukatar tikitin shugaban ƙasa karkashin inuwar jam'iyyar adawa PDP
Sokoto - Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana shirinsa na shiga tseren kujera lamba ɗaya a Najeriya a babban zaben 2023 dake tafe.
Jaridar Vangaurd ta rahoto cewa gwamnan zai nemi cikar wannan burin nasa karkashin inuwar babbar jam'iyyar hamayya PDP.
Tsohon kakakin majalisar dokokin tarayya ya sanar da kudirinsa ne da yammacin yau Litinin, bayan taron manyan masu ruwa da tsaki a Sokoto.
Da yake tabbatar da kudirinsa, Gwamna Tambuwal ya ce ba wai shirya wa ƙaɗai ya yi ba, sai dai a shirye yake ya kawo ƙarshen matsalolin da suka zame wa Najeriya ƙarfen kafa da zaran ya ɗare mulki a 2023.
Ya kuma ware kan sa daga saura ba wai a matsayin gwamna kaɗai ba, har da kujerar kakakin majalisar dokokin tarayya da ya rike ba tare da wani taɓon zargi ko cin hanci ba.
Mutum nawa ke neman takara a PDP
Tambuwal ya shiga jerin tseren tare da sauran yan takarar zama shugaban ƙasa ƙarƙashin inuwar PDP da suka haɗa da ɗan jarida, Dele Momodu, da gwamnan Bauchi, Bala Muhammed.
Kazalika, Tsohon shugaban majalisar dattawa kuma tsohon gwamnan jihar Kwara, Bukola Saraki, ya bayyana sha'awar neman takarar shugaban ƙasa.
Idan zaku iya tunawa, Tambuwal shi ne ya zo na biyu a zaɓen fidda gwani na jam'iyyar PDP a shekarar 2018, inda ya mara wa Atiku Abubakar baya.
A wani labarin na daban kuma Gwamnan PDP ya bayyana sunan wanda zai gaji kujerarsa a 2023, yace Allah ne ya masa wahayi
Gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, ya sanar da sunan ɗaya daga cikin kwamishinoninsa a matsayin wanda zai gaji kujerarsa.
Gwamnan ya sanar da kwamishinan ƙasa da albarkatun ruwa, Pasto Umo Eno, a matsyain wanda zai zama gwamna na gaba a 2023.
Asali: Legit.ng