Akwai yiwuwar APC ta kyale ‘Dan Arewa ya sake karbar tutan takarar shugaban kasa
- Jam’iyyar APC ta shiga rudun yankin da ya fi dacewa a ba dama su nemi takarar shugaban kasa
- Wasu jagororin jam’iyyar APC mai mulki sun tabbatar da cewa har yanzu ba a dauki matsaya ba
- Babu tabbacin cewa ‘dan takarar shugaban kasar da APC za ta tsaida zai fito ne daga yankin Kudu
Abuja - Alamu masu karfi sun nuna cewa jam’iyyar APC mai mulki ta samu kan ta a cikin wani irin mawuyacin hali a kan yankin da za a ba takara a 2023.
Rahoton Punch na ranar Lahadi, 30 ga watan Junairu 2022, ya nuna cewa watakila jam’iyyar APC ta bar tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a bude ga kowa.
Duk da cewa ana tunanin ‘dan takarar da APC za ta tsaida a zaben shugaban kasa zai fito daga kudu ne, jam’iyyar tana la’akari da abin da zai sa ta ci zabe.
Wasu daga cikin jagororin jam’iyyar APC sun shaidawa jaridar cewa ba a tsaida magana ba tukun.
“Duk da cewa alamu sun bayyana shugaban jam’iyya na kasa da za a zaba zai fito ne daga yankin Arewacin Najeriya, wannan ba zai hana ‘Yan Arewa neman tikitin APC ba.”
“Mu na da ‘yan takaran da suka cancanta daga yankin Arewa da Kudu. Ba mu yanke shawara ba tukuna, amma za mu dauki wanda ya fi dacewa, ya sa mu cigaba da mulki.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
- Wani jigo a jam’iyyar APC
Sai yadda ta yiwu
Da aka yi magana da wani kusa na APC daga bangaren Arewacin Najeriya, ya tabbatar da cewa ana duba duk abubuwan da za su iya yiwuwa a zabe mai zuwan.
Wannan jagora na jam’iyyar APC mai mulki ya ce idan ‘dan takarar shugaban kasa da shugaban jam’iyya su ka fito daga Arewa, za a ba shugaban APC mukami.
Idan shugaban jam’iyyar na kasa ya samu kujera a gwamnati, mataimakinsa daga kudu zai gaje shi.
Shi kuma wani babba a APC ya bayyana cewa su na sauraron abin da jam’iyyar adawa ta PDP za ta yi ne tukun, bayan nan sai NEC ta zauna idan an yi zabe na kasa.
Jonathan zai dawo mulki?
Dazu aka ji Sanata Solomon Ewuga ya fadawa Goodluck Jonathan ya yi watsi da masu ce masa ya fito takara ko kuma kimarsa ta zube idan har ya yi kunnen kashi.
Ewuga ya ce masu kiran Jonathan ya dawo fadar Aso Villa su ne wadanda suka batawa tsohon shugaban Najeriya suna a lokacin da ya gwabza da APC a zaben 2015.
Asali: Legit.ng