Shugaban Majalisa bai hakura ba, ya na ta zawarcin Gwamnonin PDP zuwa APC kafin 2023
- Shugaban majalisar dattawa na kasa, Ahmad Lawan ya kai ziyara ta musamman zuwa Akwa Ibom
- Duk da ya na PDP, Ahmad Ibrahim Lawan ya jinjinawa namijin kokarin da Udom Emmanuel ya ke yi
- Lawan ya yi kira ga Gwamna Udom Emmanuel ya fice daga jam’iyyar PDP, ya shigo APC a dama da shi
Akwa Ibom - Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ahmad Ibrahim Lawan ya yaba da aikin da ya gani wajen gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel.
Rahoton da Punch ta fitar a ranar Lahadi, 30 ga watan Junairu 2022 ya bayyana cewa Dr. Ahmad Ibrahim Lawan ya yi kira ga Udom Emmanuel ya shigo APC.
Ahmad Lawan ya kai ziyara zuwa garin Uyo, jihar Akwa Ibom ne domin kaddamar da wata cibiyar wasanni da Sanata Bassey Albert ya gina a ranar Asabar.
A wajen wannan biki, Lawan ya ajiye kunya, ya roki Mai girma Udom Emmanuel ya bar PDP.
“Ko da ba jam’iyyarmu daya ba, mu na sauraron zuwanka domin ka yi aiki da mu. Kai gwarzo ne, don haka ba za mu ji kunyar cewa ka zo ka yi aiki da mu ba.”
- Ahmad Lawan
Lawan ya yabi Sanatan Akwa Ibom
Har ila yau, shugaban majalisar dattawan kasar ya yabawa kokarin Sanata Bassey Albert, ya ce ko yaushe bai da wata magana da ta wuce ta al’ummar mazabarsa.
Lawan ya ce Bassey Albert asalin ‘dan kishin kasa ne wanda ya ke da sha’awar kawo cigaba. Albert ne mai waikltar Akwa Ibom ta Arewa maso gabas a majalisa.
“Mun zo nan ne domin mu godewa Ubangiji da ya ba mu Sanata Albert a kan aikin da ya yi a yau, wannan katafaren wuri na komai da ruwanka, ba wajen wasanni ba ne kurum, wurin daukar karatu ne.”
“Wannan wuri da aka gina ya nuna ‘yan majalisa sun fi damuwa da mutanensu domin su ne suka zabe su. Kuma mu na alfahari da duka Sanatoci uku na jihar nan.” - Ahmad Lawan.
Jaridar Vanguard ta ce dama can Ahmad Lawan da Gwamna Emmanuel abokai ne tun ba yau ba. 'Dan majalisar ya wallafa jawabin da ya yi a wajen taron a Facebook.
Lawan da zawarcin Gwamnonin APC
A can kwanakin baya, an ji cewa shugaban majalisar dattawa na kasa ya na yi wa APC zawarcin Gwamna Okezie Victor Ikpeazu. Hakan zai kara nakasa PDP a zabe mai zuwa.
Da yake jawabi wajen wani biki da aka shirya domin karrama shugaban hukumar NALDA, Lawan ya nuna cewa za su so a ce Dr. Okezie Victor Ikpeazu ya shigo jam’iyyar APC.
Asali: Legit.ng