Yadda zan bi wajen shawo kan rigingimun jam’iyya idan na zama Shugaban APC inji Sanata

Yadda zan bi wajen shawo kan rigingimun jam’iyya idan na zama Shugaban APC inji Sanata

  • Sani Musa ya bayyana irin dabarun da zai zo da shi idan ya zama shugaban jam’iyyar APC na kasa
  • Sanatan na yankin gabashin Neja a majalisar dattawa yana cikin masu neman kujerar jam’iyya
  • Musa ya ce idan ya yi nasara a zaben 2022, zai sasanta ‘ya ‘yan jam’iyya kuma ya tabbatar da doka

Abuja - Daya daga cikin manyan masu neman takarar shugabancin jam’iyyar APC na kasa, Sanata Sani Musa ya yi alkawarin magance rigingimun cikin gida.

A ranar Alhamis, 27 ga watan Junairu 2022, Vanguard ta rahoto Sanata Sani Musa yana cewa zai gyara APC idan har ya yi nasarar zama shugaban jam’iyya.

Sanatan na gabashin jihar Neja ya ce zai yi kokari wajen ganin ana bin doka da tsarin mulkin APC, sannan za a rika kiran babban taron jam’iyya bini-bini.

Kara karanta wannan

Kisan gillan Hanifa: Ministan ilimi ya yabawa kokarin da gwamnatin Kano ke yi

Da yake hira da gidan talabijin na Channels a wani shirin siyasa a yammacin Larabar nan, Sani Musa ya shaidawa Duniya manufarsa da ya yi wa lakabi da 3R.

Musa ya ce idan ya samu wannan kujera ta shugaban jam’iyya na kasa a watan Fubrairu, zai yi kokarin yin sasanci, gyaran jam’iyya da yi mata garambuwal.

Mai neman shugaban APC
Sanata Sani Musa Hoto: www.thisdaylive.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Mu na shirin maida APC ta zama tamkar hukuma; ko kamfanin kasuwanci, idan mu ka yi haka to za a rika bin duk wasu ka’idoji, sharudodi da dokoki.”
“Mu na da tsarin mulki da zai zama dole a bi shi, mu na da sharuda da za ayi aiki da shi, akwai alkawarin da mu ka yi na cin zabe da kowa sai ya cika.”
“A duk abin da mu ke yi, dole sai an rika kiran taro? Menene wannan taro? Zai kasance dole a rika yin zama a sakatariyar jam’iyya.” – Sanata Sanu Musa.

Kara karanta wannan

PDP na fuskantar barazanar ficewar dinbin mabiya kan batun tsaida ‘Dan takaran 2023

Sabani da Gwamnoni

Idan Musa ya zama shugaban APC, za a ba kowa dama a jam’iyya, kuma zai kasance dole a rika biyayya, ya ce ya san yadda zai kawo karshen matsalar gwamnoni.

Da zarar ya dare kujerar shugaban jam’iyya, Sanatan ya ce zai dinke barakar cikin gida, ya hada-kan ‘ya ‘yan jam’iyya, kuma a tabbatar ana bin doka da tsarin mulki.

A dakatar da zaben shugabanni

‘Yan tafiyar Coalition of Progressive Women in Nigeria sun bada shawarar a fasa gudanar da zaben shugabanni na kasa a wata mai zuwa ko a gamu da cikas a zabe.

Shugabar kungiyar CPWN, Cecilia Ikechukwu ta ce a hakura gangamin Fubrairu, kuma a ja-kunnen Gwamna Nasir El-Rufai da wasu manyan Gwamnonin APC biyu

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng