Rikicin APC a Kano: Zan sasanta da Ganduje amma bisa Sharaɗi ɗaya, Shekarau ya magantu

Rikicin APC a Kano: Zan sasanta da Ganduje amma bisa Sharaɗi ɗaya, Shekarau ya magantu

  • Sanatan Kano ta tsakiya kuma tsohon gwamna, Malam Shekarau yace a shirye suke su koma inuwa ɗaya da tsagin Ganduje
  • Sanatan yace za su sasanta amma bisa sharaɗin a mutunta kowane mamban jam'iyya, kuma a tabbatar masa da hakkinsa
  • Shekarau ya kuma jaddada muhimmancin sulhu a addinin musulinci, amma yace sai an yi adalci wajen aiwatar da shi a aikace

Kano - Sanatan Kano ta tsakiya kuma jagoran yan G7, Malam Ibrahim Shekarau, yace tsaginsa a shirye yake ya sasanta da tsagin gwamna Abdullahi Ganduje bisa sharaɗi.

Shekarau ya ce sharaɗin shi ne kowane mamba na jam'iyyar APC za'a tafi tare ba tare da nuna banbanci ba, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Tsohon gwamnan ya yi kira ga magoya bayan tsaginsa su kwantar da hankalinsu, domin ɓangarensa ba zai ci amanar su ba.

Kara karanta wannan

Matsayin Da Ake Ciki Akan Sulhu da yan tsagin Gwamna Ganduje, Malam Ibrahim Shekarau

Sanata Ibrahim Shekarau na jihar Kano
Rikicin APC a Kano: Zan sasanta da Ganduje amma bisa Sharaɗi ɗaya, Shekarau ya magantu Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Idan baku manta ba, kwamitin rikon kwarya na APC ta ƙasa bisa jagorancin Mala Buni da gwamna Badaru Abubakar, sun gaba da wakilan bangarorin biyu a wani yunkuri na yin sulhu ranar Talata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shekarau yace kwamitin bai yanke hukunci kan ko abu ɗaya ba, sai dai ya bukaci kowane ɓangare ya aje makaman shi domin a samu zaman lafiya.

Sanata Shekarau yace:

"Kwamitin sulhu na sane da nasarar da muka samu a kotu da kuma halin da ake ciki a jam'iyyar yanzu haka. Mun faɗa wa kwamitin a shirye muke a tattauna amma bisa sharuɗɗa."

Wane sharuɗda tsagin Shekarau ya gindaya?

Sanatan ya ce abin da tsagin su ke bukata shi ne a haɗu wuri guda kuma a tafi tare da kowa, a yi dai-daito da adalci wurin tafiyar da jam'iyya.

"Sharaɗin mu shi ne a girmama kowane mamban jam'iyya, dai-daito da adalci tsakanin kowane mamba, domin haka zai sa a baiwa kowa yancinsa."

Kara karanta wannan

Iyayen mutumin da ya kashe Hanifa sun gudu daga gidansu saboda tsoron hari

"Fafutukar da muke ba wai don mu tada yamutsi bane ko mu ci mutuncin wani, mun yi haka ne kawai don a baiwa kowa dama ya bada gudummuwarsa."
"Allah (SWA) ya jaddada muhimmancin sulhu da kyaun sa, amma ya kamata mu yi adalci, mu tabbatar da an tafi tare wajen aiwatarwa a aikace."

A wani labarin na daban kuma Yan bindiga sun tare motar kuɗi ta Banki, sun yi awon gaba da makudan kuɗaɗe

Wasu yan fashi da makami ɗauke da bindigu sun farmaki motar dakon kuɗi ta wani Banki da har yanzun ba'a gano ba.

Rahoto ya bayyana cewa maharan sun samu nasarar fasa motar, kuma sun yi awon gaba da adadi mai yawa na kuɗi a kan hanyar Otor-Owhe, ƙaramar hukumar Isoko North, jihar Delta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262