Mukarraban Buhari su na jiran matsayarsa a kan takarar Osinbajo, Tinubu a zaben 2023
- Manyan gwamnati su na sa ido domin gane inda Muhammadu Buhari ya karkata a zabe mai zuwa
- Ministoci da Hadiman Shugaban kasar su na neman wanda za su marawa baya ya yi takara a 2023
- Akwai yiwuwar Yemi Osinbajo ya rabawa Buhari hankali idan ya yi sha’awar tikiti a jam’iyyar APC
Abuja - Na-kusa da Mai girma shugaba Muhammadu Buhari su na jiran ya bayyana ‘dan takarar da yake so a cikin masu harin kujerar shi a zabe mai zuwa.
Punch ta fitar da rahoto cewa hadimai, ministoci da mukarraban shugaban kasar sun gagara marawa kowa a cikin masu neman shugaban kasa baya.
Wadannan mutane su na jiran shugaban kasa ya nuna inda ya karkata domin su san inda suka dosa.
Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa Ministoci da masu rike da manyan mukamai da ke kusa da shugaban kasa su na zura idanu domin gane ra’ayin na sa.
“Kun san shugaban kasa bai cika magana sosai ba. Za ku iya ganin yadda ya bada amsa da aka tambaye shi game da ‘dan takararsa da aka yi hira da shi.”
“Babu shugaban kasa ko gwamnan da ba zai damu da wanda jam’iyyarsa ta tsaida ya zama magajinsa ba. Dole yana da ta cewa kan wanda za a dauko.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
2007 zai maimaita kansa?
Wani gwamna mai-ci da ya ki bari a kama sunansa ya bayyana cewa shugaba Buhari ba zai fadi wanda yake so ba saboda gudun a zarge shi da fifita wani.
Rahoton ya ce haka aka yi a lokacin da Olusegun Obasanjo yake shirin barin mulki a 2007. ‘Yan siyasa suka yi ta surutansu, amma bai cewa kowa komai ba.
Watakila irin haka za a iya a zaben 2023, shugaba Muhammadu Buhari ba zai tsoma baki ba.
Za a sa Buhari a lungu
Duk da cewa Bola Tinubu ya yi maza ya bayyana niyyarsa, alamu sun nuna Buhari ya yarda da gudun ruwar Yemi Osinbajo, hakan zai iya raba masa hankali.
A lokacin da Buhari yake ganin Osinbajo ya rike masa amana, irinsu Bisi Akande na ganin cewa ya kamata ya saka alherin da Bola Tinubu yi masa a zaben 2015.
Masu neman takara a APC
A halin yanzu an ji cewa Asiwaju Bola Tinubu, David Umahi, Yahaya Bello da Orji Uzor Kalu sun fito sun nuna sha’awar neman tsayawa takarar shugaban kasa.
A makon nan aka ji tsohon gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha zai sake jarraba farin jininsa a 2023. Sanatan ya na shirin ya nemi takara ne a karkashin APC.
Asali: Legit.ng