Tseren shugabancin APC ya koma tsakanin Sanatoci 2, da tsohon Ministan Buhari

Tseren shugabancin APC ya koma tsakanin Sanatoci 2, da tsohon Ministan Buhari

  • Kusan mutane hudu ne a kan gaba yanzu wajen neman zama sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa
  • Daga cikin wadanda ke gaba a zaben akwai Sanatocin Nasarawa; Al-Makura da Abdullahi Adamu
  • Haka zalika ana ganin za a shigo da tsohon Ministan ma’adanan Najeriya, Hon. Abubakar Bwari

Abuja - Rahotannin da suke fitowa daga jaridar Daily Trust sun bayyana cewa an rage adadin masu neman kujerar shugaban jam’iyya na kasa a APC.

A wani labari da jaridar ta fitar a ranar Alhamis, 20 ga watan Junairu, 2022 an ji cewa masu harin zama shugaban APC na kasa sun koma mutane hudu.

Majiya mai karfi ta nuna shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin APC su na tunanin wanene na zaba tsakanin wasu tsofaffin gwamnoni biyu.

Kara karanta wannan

EFCC ta na binciken mutum 5 a cikin masu neman hawa kujerar Shugaban jam’iyyar APC

Wadannan tsofaffin gwamnoni duk sun yi mulki a Nasarawa, Tanko Al-Makura da Abdullahi Adamu; dukkaninsu yanzu Sanatoci ne a majalisar dattawa.

Ragowar wadanda ake hange su ne; tsohon Ministan harkokin ma’adanai, Abubakar Bawa Bwari da Saliu Mustapha wanda ya rike mukami a tsohuwar CPC.

Namen shugabancin APC
Zaben shugabannin APC na kasa Hoto: allafrica.com
Asali: UGC

Daga ina kuma

Yanzu haka Sanata Abdullahi Adamu shi ne shugaban kwamitin da ke yin sulhu a jam’iyyar APC, kuma bai fito fili ya ce yana neman wannan mukami ba.

Haka zalika shi ma Abubakar Bawa Bwari wanda ya rike Minista a gwamnatin Muhammafu Buhari, bai cikin wadanda ake ganin su na neman kujerar.

Wanene zai kai labari?

A wani kaulin, ana ganin fadar shugaban kasa ta fi natsuwa da Sanata Tanko Al-Makura wanda shi kadai ne gwamnan da Buhari ya samu a zamanin CPC.

Kara karanta wannan

2023: Ganduje, da jerin ‘Yan siyasa 10 a yankin Arewa da za su karfafi takarar Bola Tinubu

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya na ta kokarin ganin mai gidansa ya zama shugaban jam’iyya, ya na ta tuntubar wasu gwamnoni ya na masu talla.

Daga ina shugaba zai fito?

Duk da jam’iyyar APC ta na cewa ba ta tsaida yankin da za su fito neman mukamai ba, duka ‘yan takarar hudu da ake magana sun fito ne daga bangare guda.

A jiya kun samu labari cewa da alama APC za ta kasa kujerun majalisar NWC, hakan zai sa a cire Abdulaziz Yari, da Ali Modu Sheriff daga cikin 'yan takara.

A watan gobe za a san su wanene sababbin shugabannin jam’iyyar APC mai mulki na kasa. Tun a tsakiyar 2020 aka tsige Adams Oshimhole da 'yan majalisarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng