Bola Tinubu ya bayyana babban abinda zai fara yi wa Talakawan Najeriya bayan zama shugaban ƙasa a 2023
- Bola Tinubu, ya faɗi ɗaya daga cikin muhimman kudirinsa da zai fara aiwatar wa yan Najeriya da zaran ya zama shugaban ƙasa a 2023
- Tsohon gwamnan jihar Legas yace gwamnatinsa zata biya wa yara yan Sakandire kuɗin zana jarabawar WAEC
- Yace Najeriya na bukatar zaman lafiya da kwanciyar hankali matukar ana son cigaba da gina ƙasa kamar yadda kowa ke fata
Jagoran jam'iyyar APC na ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya fara bayyana wa yan Najeriya manufofinsa bayan ɗarewa karagar mulki a 2023.
A wani bidiyo da jaridar Punch ta sanya a shafinta na Facebook, Tinubu, ya ce, gwamnatinsa zata maida jarabawar WAEC kyauta ga yan Najeriya
A cewarsa, da zaran ya ɗare karagar mulki a 2023, yan Najeriya sun gama kuka kan biyan kuɗin WAEC, zai biya wa kowane ɗalibi a Najeriya.
Tsohon gwamnan jihar Legas, ya yi wannan furucin ne yayin da yake jawabi ga jiga-jigan jam'iyyar APC mata.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar ɗaya daga cikin yan takarar da suka ayyana shirinsu na maye gurbin Buhari, biyan kudin WAEC da gwamnatinsa zata yi bayan hawa mulki zai shafi kowa.
Tinubu ya ce:
"Mu zamu ɗauki nauyin biyan Kuɗin jarabawar WAEC na 'ya'yan ku, sabida haka babu wanda za'a bari a baya."
Tinubu ya faɗi abubuwan da Najeriya ke bukata
Kazalika, Tinubu, ya yi fashin baƙi kan tambarin APC da abinda hular da yake sawa ke nufi, ya kuma ƙara da wasu muhimman abubuwa da Najeriya ke bukata.
"Alamar jam'iyyar mu ta APC shi ne tsintsiya. Alamar hulata da nake sanya wa shi ne karya ƙadarin abubuwa. Kamar karya ƙadarin Talauci, jahilci da sauran su."
"Muna bukatar kwanciyar hankali a Najeriya, muna bukatar zaman lafiya da kawo ƙarshen ayyukan yan bindiga, domin mata su lamarin ya fi shafa.
"Idan babu zaman lafiya da kwanciyar hankali, ba zamu iya gina kyakkyawar ƙasar da muke mafarki ba."
A wani labarin na daban kuma Babban ɗan kasuwa a Arewa ya sanar da shugaba Buhari kudirinsa na takarar shugaban ƙasa karkashin APC a 2023
Wani ɗan kasuwa daga yankin Arewa, Moses Ayom, ya rubuta wa shugaba Buhari , wasika domin sanar da shi kudirin takara a 2023.
Ayom, ɗan asalin jihar Benuwai, ya shaida wa shugaba Buhari a wasikar cewa yana fatan maye gurbinsa ne domin ɗora wa daga inda zai tsaya.
Asali: Legit.ng