2023: Ganduje, da jerin ‘Yan siyasa 10 a yankin Arewa da za su karfafi takarar Bola Tinubu
- Bola Ahmed Tinubu yana cikin ‘yan siyasan da suka tabbatar da cewa za su nemi shiga takarar shugaban kasar Najeriya a zabe mai zuwa na 2023
- Bisa dukkan alamu, tsohon gwamnan na jihar Legas zai nemi tikitin takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC mai mulki a karshen shekarar nan
- Legit.ng Hausa ta kawo jerin ‘yan siyasan Arewa da ake tunanin za su mara masa baya wajen samun nasara a zaben fitar da gwani da babban zabe na kasa
1. Kashim Shettima
Tsohon gwamnan Borno, Sanata Kashim Shettima ya fito ya bayyana cewa yana tare da Bola Tinubu, har kuma ya yi kira ga shugaban kasa ya mara masa baya.
2. Abu Ibrahim
Abu Ibrahim wanda ya wakilci Katsina ta kudu a majalisar dattawa yana cikin manyan abokan tafiyar Bola Tinubu tun 1992, ana tunanin yana tare da shi har gobe.
3. Babachir David Lawal
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal bai taba boye biyayyarsa ga Bola Tinubu. Jigon na APC yana cikin manyan ‘yan tafiyar Tinubu a Arewa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
4. James Faleke
Hon. James Faleke mai wakiltar Ikeja a majalisar wakilai ya na cikin magoya-bayan Tinubu. Ko da yana wakiltar Legas a majalisa ne, asalin Faleke mutumin Kogi ne.
5. Lai Mohammed
Wani ‘dan siyasan da ake ganin yana tare da Bola Tinubu har gobe shi ne Alhaji Lai Mohammed. Duk da ya yi a gwamnatin Tinubu, asalinsa mutumin jihar Kwara ne.
6. Abdulmumin Jibrin
Tsohon ‘dan majalisar Kiru/Bebeji a majalisar tarayya, Hon. Abdulmumin Jibrin shi ne shugaban ‘yan Tinubu Support Management Council ta magoya-bayan Tinubu.
7. Sani Saleh
Janar Muhammad Sani Saleh mai ritaya yana cikin ‘yan siyasan Arewa da suke tare da Tinubu. Tsohon sojan ya taba zama Sanatan Kaduna a karkashin jam’iyyar CPC.
8. Babangana Zulum
Wani wanda ake tunanin zai iya marawa Tinubu baya daga Arewa shi ne gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, musamman ganin ra'ayin mai gidansa.
9. Yakubu Dogara
Irinsu shugaban tafiyar CAGG, Segun Bamgbose sun ce Bola Tinubu ya dawo da Yakubu Dogara cikin APC. Ana zargin Tinubu zai dauke shi a matsayin abokin tafiyarsa.
10. Boss Mustafa
An dade ana rade-radin cewa Boss Mustafa zai yi takara tare da Tinubu a 2023. Jiga-jigan APC kamar Umar Duhu su na ganin hakan ta na iya faruwa a zabe mai zuwa.
11. Abdullahi Umar Ganduje
Na karshe a jerin na mu shi ne gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje wanda akwai jita-jitar zai tsaya a takarar mataimakin shugaban kasa a tikitin Tinubu a APC.
A gyara dokar zabe
Shugaban majalisar wakilan tarayya, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya na ganin lokaci ya yi da za a sake kallon sharudan da aka sa wajen shiga takarar zabe a Najeriya.
Mafi karancin shaidar karatun da ake bukata wajen zama shugaban kasa shi ne takardar sakandare. Gbajabiamila ya ce za a iya wa tsarin mulki kwaskwarima.
Asali: Legit.ng