Zaben APC: Ka da ku raina mana hankali fa – Kungiyar PGF ta fadawa su Mala Buni
- Shugaban kungiyar Progressive Governors’ Forum, Salihu Mohammed Lukman ya caccaki CECPC
- Darekta Janar na PGF ya maidawa kwamitin rikon kwarya martani kan shirin zaben shugabanni
- A jiya John James Akpanudoedehe yake cewa ana zantawa da masu ruwa da tsaki a kan shirin zaben
Abuja - Darekta Janar na kungiyar Progressive Governors’ Forum, Salihu Mohammed Lukman, yace an maida gwamnoni tamkar ba koman komai ba.
Jaridar Daily Trust ta ce Malam Salihu Mohammed Lukman ya yi kaca-kaca da kwamitin rikon na jam’iyyar APC da su Mai Mala Buni su ke jagoranta.
Kamar yadda muka samu wani rahoto, Lukman ya fitar da jawabi na musamman a ranar Alhamis, 13 ga watan Junairu, 2022 a birnin tarayya Abuja.
Shugaban kungiyar ta PGF ya na ganin bai kamata kwamitin Buni ya raina hankalin gwamnoni ba.
PGF ta yi wa CECPC raddi
Sanarwar ta PGF ta na zuwa ne bayan sakataren riko na APC, John James Akpanudoedehe ya ce ana tattaunawa kafin a shirya zaben shugabanni na kasa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da yake maida masa martani, The Eagle ta rahoto Lukman yana cewa bai kamata Sanata John James Akpanudoedehe ya yi wannan maganar da ya yi ba.
‘Dan siyasar yake cewa da zarar matsala ta taso a APC, sai a fito ana zargin gwamnonin jihohi ne, alhali sam gwamnonin ba za su sabawa shugaban kasa ba.
Kwamitin CECPC ya daina yi wa gwamnoni sharri
“Kwamitin CECPC ya daina ikirarin yana jiran ayi taron gwamnonin APC kafin ya dauki matakan da suka kamata domin shirin yin babban zaben shugabanni.”
“Wannan ikirari ba gaskiya ba ne, kuma ana kokarin a ci banzar goyon bayan gwamnoni, don haka aka raina gwamnonin APC a kan duk abin da ke faruwa.”
“Gwamnonin APC kamar sauran ‘yan jam’iyya ba za su cusa kan su a duk wani abin da zai iya jawowa a ci mutuncin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba.”
A karshe, Lukman ya bukaci CECPC su daina yi wa al’umma karyar ana wata tattaunawa da masu ruwa da tsaki, domin an gama wata tattaunawa tun a bara.
Mu na jiran Omo-Agege - kungiya
A ranar Alhamis ne aka ji wata kungiya mai suna Enyen-Nyen Movement a jihar Delta ta na so Ovie Omo-Agege ya yi takarar gwamna a zabe mai zuwa na 2003.
Kungiyar ta na ganin Sanatan ya fi kowane ‘dan takara dacewa da gwamnan Delta musamman yadda aka yi rashin dace, su ka gaza samun shugaba na kwarai.
Asali: Legit.ng