Tseren Tikiti: Jam'iyyar APC ta bayyana gwamnan da zata goyi baya ya gaji shugaba Buhari a 2023

Tseren Tikiti: Jam'iyyar APC ta bayyana gwamnan da zata goyi baya ya gaji shugaba Buhari a 2023

  • Jam'iyyar APC ta nuna goyon bayanta 100 bisa 100 kan takarar gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi a zaben 2023
  • Shugaban APC reshen jihar Ebonyi, Mista Emegha, yace matukar gwamnansa ya zama shugaban ƙasa, to Najeriya zata yi gogayya da sauran ƙasashe
  • Ya kuma yi kira ga yan Najeriya daga kowane bangaren ƙasar nan su goyi bayan gwamna Umahi ya cika burinsa a 2023

Ebonyi - Jam'iyyar APC reshen jihar Ebonyi, ranar Laraba, tace nasarorin gwamna David Umahi, a shekaru 6 da suka wuce kaɗai sun isa su bashi nasara ya zama shugaban ƙasa a 2023.

Punch ta rahoto Shugaban APC reshen jihar, Chief Stanley Okoro-Emegha, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai a Abakaliki, yayin da yake tsokaci kan kudirin gwamna.

Kara karanta wannan

Bayan sanar da Buhari, Gwamnan APC ya bayyana dalilin da yasa zai gogayya da Tinubu a 2023

Haka nan kuma ya jinjina wa gwamna Umahi bisa bayyana manufarsa ta takarar shugaban ƙasa a zaben dake tafe.

David Umahi, gwamnan jihar Ebonyi
Tseren Tikiti: Jam'iyyar APC ta bayyana gwamnan da zata goyi baya ya gaji shugaba Buhari a 2023 Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A cewar Mista Emegha, kudirin gwamna na shiga tseren tikitin shugaban ƙasa, wata babbar nasara ce da cigaba ga jiharsu da yankin kudu baki ɗaya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma nuna yaƙininsa cewa matukar Umahi ya zama shugaban ƙasa, to zai kawo manyan ayyukan raya ƙasa a Najeriya da kuma mutanen cikinta duba da nasarorinsa a matsayin gwamna.

Shugaban APC yace:

"Ina mai sanar da yan Najeriya na gida da waje cewa bayyana kudurin shiga tseren tikitin shugaban ƙasa da gwamna Umahi ya yi, shi ne abu mafi alheri da ya faru a Najeriya duba da halin da ake ciki."
"Kamar yadda ya shaida wa Channels TV, inda ya yi alƙawarin kwatanta ayyukan da ya yi a Ebonyi, idan ya kai matakin ƙasa. Gwamnan mu ba ya goyon bayan kowa sai kansa."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gwamnan APC ya sanar da shugaba Buhari kudirinsa na takara a zaben 2023

"Waɗan da suka san jihar Ebonyi kafin zuwan Injiya David Umahi sune zasu yanke hukunci. Karkashin Umahi, Ebonyi ta samu cigaban da take gogayya da ƙasashen da suka cigaba."

Ya samu nasara a bangaren tsaro

Shugaban APC a Ebonyi ya ƙara da cewa, bayan haka gwamna bai tsaya nan ba, ya yi kokarin samar da dawwamammen zaman lafiya tsakanin mutane.

"Ina kira ga yan Najeriya su jingine banbancin addini ko kabila, Dan allah su mara wa takarar David Umahi baya domin ya cimma mafarkansa na zama shugaban ƙasa."

A wani.labarin kuma Jam'iyyar PDP ta bayyana mutanen da take zargin suna da hannu a ta'addancin yan bindiga a Najeriya

Babbar jam'iyyar hamayya PDP ta yi kira ga hukumomin tsaro su gayyaci shugabannin APC domin amsa tambayoyi kan zargin alaƙa da yan ta'adda.

A cewar PDP, akwai bukatar jagororin APC su yi karin haske bisa rahoton shigo da yan ta'adda cikin ƙasar nan da kuma kyale su, suna aikata ta'addanci kan yan Najeriya.

Kara karanta wannan

2023: Ƴan Najeriya na son PDP ta karɓi shugabancin ƙasa daga hannun APC, Wike

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262