Da Dumi-Dumi: Gwamna mai ci ya sanar da shugaba Buhari kudirinsa na takarar shugaban ƙasa a 2023
- Gwamna David Umahi, na jihar Ebonyi, yace ya faɗa wa shugaban ƙasa Buhari, shirinsa na neman kujerar shugaba a 2023
- Umahi, yace bai taba goyon bayan kowa ba game da shugabancin Najeriya a 2023, don haka kansa kawai yake goyon baya
- Yace Buhari ya nuna masa ya zama wajibi ya nemi shawarin shugabanni daga kowane sashin ƙasar nan
Abuja - Awanni 24 bayan jagoran APC, Bola Tinubu, ya sanar da shugaba Buhari shirinsa na takara, Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi, ya faɗa wa Buhari na shi kudirin a 2023.
Vanguard ta ruwaito cewa gwmana Umahi ya sanar da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, kudirinsa na neman kujerar shugaban ƙasa a babban zaɓen dake tafe.
Umahi ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labaran gidan gwamnati, jim kaɗan bayan ganawar sirri da shugaba Buhari ranar Talata.
Gwamnan yace ya sanar da shugaba Buhari kamar yadda jagoran APC na ƙasa, Bola Tinubu ya yi, wanda ya bayyana sha'awarsa ranar Litinin a gidan gwamnati.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya kara da cewa shugaban kasa ya faɗa masa ya yi shawara da mutane sosai kan kudirin na shi, kammar yadda Daily Trust ta rahoto.
Ba na goyon bayan kowa sai kaina - Umahi
Gwamna Umahi ya bayyana cewa bai taɓa nuna goyon bayan kowa ba a takarar shugaban ƙasa, don haka kan shi kawai yake goyon baya.
Da aka tambaye shi abin da ya kai shi wurin shugaba Buhari, Umahi yace:
"Mun tattauna kan siyasa, cigaban jam'iyyar mu ta APC a Najeriya da kudu maso gabas. Da kuma bukatar yan yankin Kudu Maso Gabas kan kujerar shugaban ƙasa."
Gwamnan ya yi ikirarin cewa matukar APC ta amince ta kai tikitin takara kudu maso gabas, ba shakka nasarorin da ya samu a shekara 6 zai ba shi damar samun tikiti.
Babbar Magana: Jam'iyyar APC ta maida zazzaafan martani ga kalaman Tinubu na takarar shugaban ƙasa a 2023
"Shugaba Buhari ya amince cewa duk wanda ke son neman takara to ya zurfafa shawara kuma ya ziyarci dukkan shugabanni."
A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP ta bayyana mutanen da take zargin suna da hannu a ta'addancin yan bindiga
Jam'iyyar PDP ta bukaci hukumomin tsaro su kira shugabannin APC mai mulki domin amsa tambayoyi kan alaƙa da yan ta'adda.
PDP tace bai kamata jami'an tsaro su kyale ikirarin da tsohon jigon APC ya yi ba kan shigo da yan ta'adda Najeriya a 2015.
Asali: Legit.ng