An yi wa Hadimin Shugaban kasa rubdugu saboda yace sai nan gaba za a ga amfanin Buhari
- Bashir Ahmaad, ya ce ’yan Najeriya ba za su ga amfanin mulkin Muhammadu Buhari a yanzu ba
- Mai ba shugaba Muhammadu Buhari shawara ya ce sai bayan kammala wa’adinsa za a ci moriya
- Mutane sun yi wa Ahmaad ca bayan wannan magana da ya yi a kafar sada zumunta na Facebook
FCT, Abuja - Mai taimakawa Muhammadu Buhari a harkar kafofin sadarwa na zamani, Bashir Ahmaad yace sai nan gaba za a ga amfanin shugaban kasar.
Bashir Ahmaad ya fito shafinsa na Facebook inda yake cewa Mai gidansa watau Mai girma Muhammadu Buhari ya daura Najeriya a kan turba ta kwarai.
Da yake magana a Facebook a ranar Litinin 10, ga watan Junairu, 2022, Ahmad, ya ce jama’a za su ci moriyar gwamnatin Muhammadu Buhari ne a nan gaba.
“Turbar da Shugaba Buhari ya ɗauka ba za a ga amfaninta a fili a yanzu ba sai bayan ya bar mulki.”
“Ya ɗora ƙasar nan a kan kyakkyawan tsarin da duk shugaban da ya zo zai ɗora.”
“Wasu tsare-tsaren na gyara ba sa iyuwa sai an sha wuya, amma kuma daga ƙarshe za a ci moriyarsu na dindin-din.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
- Bashir Ahmaad
Jaridar Aminiya tace Hadimin ya yi wannan jawabi ne bayan suka da shugaba Buhari ya sha, game da hirarsa da ya yi a gidan talabijin na Channels.
An yi wa Bashir Ahmaad raddi
Sai dai tuni wasu suka fara maida masa martani a shafin na sa. Legit.ng Hausa ta tattara abin da wasu daga cikin masu bibiyar Malam Ahmaad suke fada.
Irinsu Idris Hamza Yana sun bukaci hadimin shugaban Najeriyar ya yi dogon rubutu dauke da hujjoji ta yadda zai gamsar da ‘yan adawa kan inda ya dosa.
“Da zai sauka tun yanzu mufara ganin dadin idan yaso ko bayan wata shida ne sai ya dawo ya qarasa abunda ya rage masa.”
- Khalifa Abubakar
“Wallahi Malam Bashir Ahmad don dai kaine kayi wannan posting din kawai.”
- Shehi M Salga
“Dama abinda ake biyanka kenan danshi...”
- Abubakar A. Idris
“Duk hankali da tunanin masu tunani basu hango hakaba.”
- Anas Dan Aunai
“Sata ce har yanzu ana yin ta, Magu, Babachir and co duk watayawa suke abinsu.”
- Muhammad Salim Ismail
“Bashir Ahmad kuji tsoron Allah a maganar ku.”
- Ibrahim Mairiga
“Mara tsoron Allah ne kaɗai zai yarda da wannan soki-burutsun."
"Baba ai ya gama lalata mana tattalin arziki.”
- Mukhtar Yunusa Idris
Asali: Legit.ng