Babban taro: Gwamnonin APC za su gana da Shugaba Buhari don tsayar da rana
- Gwamnonin APC na shirin ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan babban taron jam'iyyar mai zuwa
- Shugaban kasa da gwamnonin za su shiga labule ne a ranar Lahadi, 9 ga watan Janairu domin tsayar da ranar gudanar da babban taron a watan Fabrairu
- Gwamna Simon Lalong na jihar Filato ne ya sanar da hakan a ranar Juma'a, 7 ga watan Janairu
Gwamnonin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sun shirya tsaf domin ganawa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Lahadi, domin tsayar da rana don babban taron watan Fabrairu, Channels TV ta rahoto.
Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ne ya bayyana hakan ga manema labarai na fadar shugaban kasa bayan ganawa da shugaban kasar a ofishinsa a ranar Juma'a, 7 ga watan Janairu.
A cewarsa, shugaba Buhari ya bayar da tabbacin cewa babu abun da zai hana APC gudanar da taron a watan Fabrairu, rahoton Sahara Reporters.
Ya kara da cewa saboda haka dukka gwamnonin suka yanke shawarar haduwa da daidaita duk wani ra’ayin a ranar Lahadi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kan yanayin tsaro a kasar, Gwamna Lalong ya jaddada cewa lamarin garkuwa da mutane a kasar ya ragu.
Hakazalika, ya bayyana cewa ya matsu ya ga jiragen yaki da aka kawo sun fara aiki ba ji ba gani kafin tsakiyar shekarar.
Sabon rikici ya kunno kai a APC yayin da fusatattun mambobin jam’iyyar suka maka Buni a Kotu
A gefe guda, mun ji cewa rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar All Progressives Congress (APC) kan babban taron watan Fabrairu ya kara kamari.
Jaridar Punch ta rahoto cewa wasu mambobin jam'iyyar sun maka kwamitin riko wanda Mai Mala Buni ke jagoranta a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja.
Masu karar sun nemi umurnin kotu don dakatar da kwamitin da Buni ke jagoranta daga gudanar da babban taron.
Asali: Legit.ng