Gwamnan APC ya gano ana 'makarkashiya' domin bata masa suna a takarar Shugaban kasa

Gwamnan APC ya gano ana 'makarkashiya' domin bata masa suna a takarar Shugaban kasa

  • Kayode John Fayemi yace akwai wasu da suke kokarin ganin bayansa a siyasa saboda hassada
  • Gwamnan jihar Ekiti ya bayyana wannan ne a wani jawabi da hadiminsa, Yinka Oyebode ya fitar
  • Yinka Oyebode yace ana shirin batawa Mai gidansa suna domin ana tunanin zai yi takara a 2023

Ekiti - Mai girma Dr. Kayode John Fayemi na jihar Ekiti yace ya tsonewa wasu ido a jam’iyyar APC saboda nasarorin da yake samu a tafiyar siyasa.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa . Kayode John Fayemi ya bayyana haka a wani jawabi ta bakin babban sakataren yada labaransa, Mr. Yinka Oyebode.

Da yake bayani a jawabin a ranar Alhamis, 6 ga watan Junairu, 2021, gwamnan Ekiti yace akwai kokarin da ake yi na bata masa suna a wajen al’umma.

Kara karanta wannan

Matan Arewa sun bayyana sunan gwamnan da suke kaunar ya gaji Buhari a zaben 2023

Oyebode yace ana yunkurin yin hakan ne saboda Kayode Fayemi ya rasa karbuwa wajen jama’a.

Jawabin gwamnatin Ekiti

“Ana sanar da jama’a cewa akwai danyen shirin da wasu ‘yan siyasa suka kitsa domin a bata sunan gwamnan jihar Ekiti, shugaban kungiyar gwamnoni, Dr Kayode Fayemi.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Kamar yadda aka bankado, tuggun wasu marasa nauyi a ma’aunin siyasa da wadanda suka rasa makama ne a fadin kasar nan ne suka shirya bata sunan gwamnan Ekiti.”
Gwamnan Ekiti
Gwamna Fayemi da Shugaba Buhari Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

“Abin da suke so shi ne suyi amfani da wasu kungiyoyi da ba a san su ba, su bata Gwamna Fayemi, ayi masa tabo ta yadda ba zai samu karbuwa ba a duk fadin kasar nan.”
“Wannan yana cikin shirinsu na zaben shugaban kasa a 2023.” - Yinka Oyebode.

Punch ta rahoto Oyebode yana mai cigaba da cewa babu inda Fayemi ya fadawa wani cewa zai yi takarar shugaban kasa duk da doka ba ta hana shi ba.

Kara karanta wannan

Zamfara: Jam’iyyar APC ta yi fallasa, tace wani tsohon Soja yana da alaka da ‘Yan bindiga

Har ila yau, a jawabin da hadimin gwamnan ya fitar dazu, yace kaddarar Fayemi ta na wajen Ubangiji, amma yanzu rikon jihar Ekiti ya sa a gabansa.

A karshe Oyebode yace wadannan ‘yan adawa na bakin cikin yadda Fayemi har ya zama gwamnan gwamnoni, don haka suke yi masa bakin-ciki.

Rikicin APC a Gombe

A jiya ne aka ji cewa shugaban kwamitin rikon kwaryan APC, gwamnan jihar Yobe, Mai Mai Mala Buni ya kawo karshen rikici da ake yi a reshen jihar Gombe.

Gwamna Mai Mala Buni ya sasanta Sanata Mohammed Danjuma Goje da Gwamna Inuwa Yahaya. An yi sulhun ne a gidan Sanatan Nasarawa, Abdullahi Adamu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel