Bayan wata da watanni ana rigingumu, Mai Mala Buni ya sasanta rikicin APC a jihar Gombe

Bayan wata da watanni ana rigingumu, Mai Mala Buni ya sasanta rikicin APC a jihar Gombe

  • Shugaban kwamitin rikon kwaryan APC, Mai Mala Buni ya kawo karshen rikici da ake yi a Gombe
  • Gwamna Mai Mala Buni ya sasanta Sanata Mohammed Danjuma Goje da Gwamna Inuwa Yahaya
  • Hadimin gwamnan Gombe, Ismaila Uba Misilli ya tabbatar da labarin wannan sulhu da aka yi a Abuja

Abuja - Shugaban kwamitin rikon kwarya na APC, Mai Mala Buni yace an sulhunta gwamnan jihar Gombe, Alhaji Inuwa Yahaya da Mohammed Danjuma Goje.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Gwamna Mai Mala Buni yana cewa an dinke barakar da ke tsakanin Mai girma Inuwa Yahaya da Sanata Mohammed Danjuma Goje.

Legit.ng ta rahoto maku cewa an dade ana ta samun sabani tsakanin bangaren gwamna Yahaya da na tsohon gwamnan Gombe kuma Sanata mai-ci, Danjuma Goje.

Jagororin jam’iyyar APC sun zauna da Inuwa Yahaya da Sanata Goje ne a gidan shugaban kwamitin sulhu da aka kafa, Sanata Abdullahi Adamu a garin Abuja.

Kara karanta wannan

Jerin fitattun Sanatoci 10 da suka ci zaman benci a Majalisar Dattawa a shekarar 2021

Tsohon shugaban majalisar wakilan tarayya, Rt. Hon. Yakubu Dogara, da wasu Sanatoci suna cikin wadanda aka yi zaman sulhun da su a ranar Laraba da yamma.

APC a jihar Gombe
Inuwa Yahaya, Mohammed Danjuma Goje da Mala Buni Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Vanguard ta ce tsohon gwamnan Borno, Sanata mai-ci, Kashim Shettima da tsohon gwamman Enugu, Sullivan Chime su na cikin wadanda aka yi taron da su a jiya.

Darekta Janar na harkokin yada labarai na gwamnan jihar Yobe, Malam Mamman Mohammed yace an yi nasarar sulhunta bangarorin biyu a wannan zaman da aka yi.

“Zaman sasancin da aka yi ya tabbatar da karfin ikon jam’iyya a jihar.”
“Jam’iyya za ta cigaba da neman hanyoyin sulhu, ta sasanta masu ruwa da tsaki a fadin kasar nan domin a samu hadin-kai da za a fuskanci zaben 2023.” – Mohammed.

Kara karanta wannan

Kwanan nan Sojoji za su ga karshen Turji – Gwamnan Sokoto ya yi albishir a 2022

A wani jawabi da mai magana da yawun bakin gwamnan na Gombe, Ismaila Uba Misilli ya fitar, yace an yi taron ne domin a kawo karshen rigingimun cikin gida.

Jonathan zai dawo?

A jiya ne Hon. Abdurrahman Kawu Sumaila ya soki masu neman a ba Dr. Goodluck Jonathan takara a APC, yace ya kamata a kyale tsohon shugaban kasar ya huta.

Tsohon ‘dan majalisar tarayya mai wakiltar Takai da Sumaila yace duk da Jonathan ya fi wasu 'yan siyasar da yawa inganci, amma APC ba ta rasa ‘yan takararta ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng