Kwankwaso ya fitar da magoya daga duhu kan batun barin PDP da neman Shugaban kasa
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya tanka masu rade-radin cewa zai bar jam'iyyar hamayya ta PDP
Jita-jitar da ake yadawa ita ce tsohon gwamnan zai sauya zuwa jam'iyyar APC mai mulki kafin 2023
Tsohon Sanatan Kano ta tsakiya yace zai sanar da jama’a idan ya yanke shawarar neman mulkin kasa
Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana mai gamsarwa game da rade-radin da ake ji na cewa zai sauya sheka.
A wata hira da DW Hausa tayi da shi a ranar Laraba, 5 ga watan Junairu, 2022, Rabiu Musa Kwankwaso yace babu gaskiya a jita-jitar da ke faman yawo a gari.
Rabiu Musa Kwankwaso wanda ya yi mulki sau biyu a jihar Kano, yace a halin yanzu bai yi wani zama da wasu a kan shirin komawa jam’iyyar APC mai mulki ba.
A cewar Sanata Kwankwaso, ba yau aka saba yada irin wannan jita-jita ba, yace bini-bini a kan fito ana karyar yana shirin ficewa daga jam’iyyar hamayya ta PDP.
Kwankwaso zai sauya-sheka?
“Maganar canza-sheka, babu ita. A yanzu dinnan ba na magana da wasu mutane na cewa zan koma (zuwa jam’iyyar APC).”
Amma tun kafin wannan lokaci, mutane suke ta yin jita-jita. Amma duk lokacin da jita-jitar ta taso, sai ka ga mutane sun yarda.”
“Sai a ce ‘Ai Kwankwaso gobe zai koma, rana irinta yau zai koma, wata mai zuwa zai koma. Idan an zo an wuce, sai a sake shigo da wata.”
- Rabiu Kwankwaso
Takara a zaben 2023
Har ila yau, DW tayi wa tsohon Ministan tsaron tambaya ko ya na da niyyar tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023, inda yace bai kai ga yanke shawara ba.
“Ba mu gaggawa, sai an yi Nazari, sai an taba mutanen da ya dace (masu hakki a kan al’amarin.”
“Idan Allah ya kai mu wannan lokaci, idan Allah ya yarda za mu sanar da ku game da matakin da Kwankwaso zai dauka game da abin da ya shafi zabe na 2023.”
Rade-radi su na ta karfi
A baya an ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya amsa wannan tambaya ta komawa jam'iyyar APC da kan sa a wata doguwar hira da ya yi kwanaki.
Kwankwaso ya bayyanawa manema labarai cewa a harkar siyasa komai ya na iya faruwa, ya kuma bayyana cewa burinsa shi ne a samu shugaba na kwarai.
Asali: Legit.ng