Aikin da ke gaban Dr. Iyorchia Ayu kafin jam’iyyar PDP ta iya doke APC a zaben 2023
- Yayin da aka fara shirye-shiryen zaben 2023, jam’iyyar PDP za ta so tayi waje da APC mai mulki
- Sai shugabannin PDP sun yi da gaske kafin su iya sake karbe ragamar shugabancin Najeriya a 2023
- Idanu su na kan sabon shugaban jam’iyyar hamayyar, Dr. Iyorchia Ayu domin ya kai PDP ga nasara
Daily Trust ta kawo abubuwan da ya kamata Ayu ya yi tsakanin yanzu da 2023:
1. Zaben fitar da gwani
Zaben tsaida da ‘dan takara da jam’iyyar PDP za tayi ya na cikin abubuwan da za su taimakawa PDP wajen samun nasara a babban zaben da za ayi a 2023.
Wadanda ake ganin za su nemi tikitin shugaban kasa a 2022 sun kunshi Atiku Abubakar, Aminu Tambuwal, Bukola Saraki da irinsu Rabiu Musa Kwankwaso.
2. Yankin da za a kai takara
Wata matsala da sai Dr. Iyorchia Ayu da ‘yan majalisarsa sun yi da gaske shi ne tsaida yankin da PDP za ta fito da ‘dan takara tsakanin yankin Kudu da Arewa.
3. Sauya-sheka
Legit.ng ta na ganin cewa akwai bukatar shugabannin jam’iyyar PDP su yi bakin kokarinsu wajen hana kusoshin jam’iyya canza-sheka, yin hakan zai iya lahanta su a zabe.
4. Zabukan gwamnoni da za a yi
Idan PDP ta na so ta samu kwarin-gwiwa a zaben 2023, dole ta iya karbe jihohin Osun da Ekiti a bana, wanda yanzu haka su na hannun jam’iyyar APC mai mulki.
5. Rikicin cikin gida
Kafin PDP ta shiga takarar shugaban kasa a zaben na 2023 dole sai an magance duk wasu rikicin cikin gida da ake fama da su a jihohin da ake fama da rigingimu.
6. Shari’ar Uche Secondus
Ya zama dole jam’iyyar PDP ta san yadda za ta sasanta da tsohon shugabanta na kasa, Prince Uche Secondus wanda yanzu ya shigar da kara a gaban kotun koli.
Jonathan zai dawo?
An ji cewa Dr. Goodluck Jonathan ya yi zaman kus-kus da wasu daga cikin manyan jagororin da ke yi masa yakin zabe domin ya sake komawa kan karagar mulki.
Akwai magoya bayan da suke sha’awar ganin Jonathan ya sake komawa kujerar shugaban kasa.
Asali: Legit.ng