Komai ya na iya faruwa a 2023 – Kwankwaso ya tanka masu rade-radin sake shiga APC
Rade-radi su na ta yawo a game da sauya-shekar Rabiu Musa Kwankwaso daga PDP zuwa jam’iyyar APC
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya amsa wannan tambaya da kan sa a wata doguwar hira da ya yi kwanan nan
Punch ta tambaye shi ko da gaske ya na shirin shiga APC idan an karbe ta daga hannun Abdullahi Ganduje
Abuja - Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyanawa Punch cewa a harkar siyasa komai ya na iya faruwa, ya kuma bayyana akidarsa da irin burinsa.
Hadimin 'dan siyasar, Saifullahi Muhammad Hassan ya tsakuro wannan hira a shafinsa na Facebook.
“A siyasa komai mai iya yiwuwa ne. Ba mu bukatar makiya na din-din-din, abin da muke so shi ne masoya na din-din-din, wannan na da muhimmanci.”
“Masoya mu ke nema, zai ba ka sha’awa cewa a cikin wadanda muka fara siyasa da su shekaru 30 da suka wuce, wasu su na raye, kuma mu na nan tare.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Har ma wadanda suka rasu shekaru 30 da suka wuce zuwa yanzu su na cikin ranmu, shekara- shekara mu kan samu danginsu, mu yi masu wani abu.”
“Saboda haka a zaben 2023, na yi imani cewa abubuwa da yawa za su iya faruwa.” – Kwankwaso.
Sai yadda kotun koli tayi da PDP
A game da komawa jam’iyyar APC da ya bari a 2018, tsohon Sanatan na Kano ta tsakiya yace a halin yanzu makomar jam’iyyar PDP ta na ga kotun koli.
“PDP ta shirya zaben shugabanninta, shakka-babu tsohon shugaban jam’iyya na kasa, Uche Secondus ya na kotu, kuma kotun koli za ta yi hukunci.”
“Hukuncin da kotun koli za tayi kwanan nan zai yi tasiri a kan makomar jam’iyyar (PDP). Haka zalika matakin da shugabannin jam’iyya suka zartar.”
- Kwankwaso
Kwankwaso wanda yayi gwamna sau biyu a Kano yace jam’iyya ta na iya biyewa gwamnoninta 13, tayi watsi da maganar duk sauran ‘ya ‘ya da magoyanta.
A gefe guda kuma, ‘dan siyasar ya bada shawarar cewa a ajiye girman kai, a tafi da kowa, yace wannan shi ne zai taimakawa jam’iyyun siyasa a wajen zabe.
A cewar Kwankwaso, ita ma APC ta na yin irin na ta shirin wanda idan tayi kuskure za ta auka cikin rigimar da ta fi ta PDP, yace burinsa a samu shugaba na gari.
Mu na lale da Kwankwaso - Babafemi Ojudu
A jiya ne aka ji Hadimin shugaban kasa, Babafemi Ojudu yace zuwan Kwankwaso APC zai amfane su domin shi gawurtaccen ‘dan siyasa ne mai jama’a tare da shi.
A gefe guda, Mai magana da yawun bakin tafiyar Kwankwasiyya, Sunusi Bature Dawakin Tofa yace jita-jitar sauya-shekan duk ba su da asali ko tushen kamawa.
Asali: Legit.ng