Gwamna ya sallami hadiminsa kan rubutun rashin kunya Facebook
- Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta ya kori hadiminsa bisa abin da ya kira rashin sanin aiki da kuma rashin kunya
- Rahoto ya nuna cewa, Mista Oghenesivbe, ya rasa aikinsa ne bayan wani rubutun rashin ɗa'a da ya yi a dandalin facebook
- Gwamnan ya umarce shi ya bi duk matakan da ya dace wajen mika kayayyakin gwamnati ga sakataren dindindin na gidan gwamnatin jiha
Delta - Gwamnan jigar Delta, Ifeanyi Okowa, a ranar Alhamis, ya sallami mai taimaka masa ta bangaren sadarwa, Latimore Oghenesivbe.
Punch ta rahoto cewa gwamnan ya ɗauki wannan matakin sabida abin da ya kira, "Rashin kunya da rashin ɗaukar aiki da muhimmanci."
Wannan na ƙunshe ne a wata takarda mai ɗauke da kwanan watan 29 ga watan Disamba, 2021 kuma sakataren gwamnati ya rattaba hannu a akai.
Meyasa gwamnan ya sallame shi?
Tsohon hadimin gwamnan, Oghenesivbe, ya yi zargin cewa uban gidansa ba ya masa adalci a tswon shekaru biyar da suka yi aiki tare.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya kara da cewa gwamnan na zagaye da wasu mutane waɗan da suka maida shi mara kula da adalci a al'amuransa, kamar yadda Tribune ta tahoto.
A wani rubutu da ya yi a shafin Facebook, wanda ake ganin shi ne ya jawo masa rasa mukaminsa, Oghenesivbe, yace an hana shi wasu garabasa da aka baiwa abokan aikinsa na sashin sadarwa a gwamnatin jihar.
Yace ya karbi buhun shinkafa mai nauyin kilo 25 guda biyu da kuma kudi N50,000 daga cikin miliyan N25m da Okowa ya tura wa tawagarsa ta bangaren sadarwa.
Gwamna bai ji daɗin kalamansa ba
Amma a takardan sallama gwamna Okowa ya nuna rashin jin dadinsa bisa abin da hadimin nasa ya yi, inda yace, "Akwai rashin kunya da rashin giramamawa a ciki."
"Ba zamu lamurci irin haka ba, ina bakin cikin sanar maka da cewa ba mu bukatar aikin ka, kuma mun sallame ka."
"Ina mai umartan ka da ka bi duk wasu matakai na mika dukkan wasu kayayyakin gwamna ga sakataren dindindin na gidan gwamnati."
A wani labarin kuma Gwamnatin shugaba Buhari ya bayyana babban kalubalen da ya hana ta sukuni a shekarar 2021
Ministan yada labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, yace matsalar tsaro ta zama karfen kafa ga gwamnatin shugaba Buhari a shekarar nan.
A cewarsa duk da waɗan nan matsaloli da kuma kwan gaba kwan baya da tattalin arziki ke yi, Buhari ya samu nasarori da dama a 2021.
Asali: Legit.ng