Masu garkuwa da mutane sun sa ya sauka daga motar Buhari, ya shiga darikar Kwankwasiyya
- Sirajo Saidu Sokoto ya fito shafinsa na Facebook ya na bada sanarwar sauka daga motar Buhariyya
- Dalilin wannan mutumi na yin haka daya ne, an yi garkuwa da ‘yanuwansa, babu wanda ya taimaka masa
- Malam Sirajo Saidu Sokoto yace daga yanzu ya koma tafiyar Kwankwasiyya ta Rabiu Musa Kwankwaso
Sokoto - Wani Bawan Allah mai amfani da Facebook, mai suna Sirajo Saidu Sokoto ya bayyana cewa ya daina goyon bayan shugaba Muhammadu Buhari.
Malam Sirajo Saidu Sokoto ya fito kan shafinsa ya bayyana riddarsa daga tafiyar Muhammadu Buhari, yace ya koma goyon bayan tafiyar Kwankwasiyya.
Da yake bayanin sauya-shekarsa a siyasa, Sirajo Sokoto yace ya shiga tsarin Kwankwasiyya ne a sakamakon dauke wasu ‘yanuwasa da ‘yan bindiga suka yi.
Duk da ya na cikin masu kare gwamnatin Buhari a shafukan sada zumunta, Sokoto yace ba a taimaka masa a lokacin da aka yi garkuwa da ‘yanuwansa ba.
A cewar Siraju Saidu Sokoto ko da ya yi ta sanar da jama'a, amma har danginsa suka biya kudin fansar ‘yanuwansa da aka dauke, ba a ba shi gudumuwa ba.
Jawabin Siraju Saidu Sokoto a Facebook
“Yau-Wed (Laraba) 29-12- 2021. "Ni Sirajo Sa idu Sokoto.
"Na Bar Tafiyar Buhariya. "Na Koma Tafiyar Kwankwasiyya.”
"Sanadiyar Barayi Sun Yi Garkuwa Da 'Yan Uwana 5. "
"Nayi Ta Postin Ina Sanarwa! "
Amma Har Muka Biya Kudin Fansa, ba a Taimakan Ba!" - Sirajo Saidu Sokoto
Abubuwa sun canza a 'yan kwanaki
A baya, Sirajo Saidu Sokoto ya nuna yadda yake kaunar Buhari, har a ‘yan kwanakin nan ya fito yana cewa ya na jin dadin ganin shugaban kasar ya na murmushi.
Tuni dai har wannan mutum ya fara daura hotunan Madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso domin nuna inda ra’ayin na sa ya karkata yanzu.
Martanin mutane a dandalin Facebook
Mutane na ta maida martani ga wannan Bawan Allah a Facebook tun da ya bada wannan sanarwa.
"Allah ya kiyaye. Sai dai kwankwasiyya ba a bada kudi tsarine na tsayawa akan gaskiya da rokon amana Allah ya bamu sa'a."
- Auwalu Inuwa Ma’aruf
"Anya Ka sanar da Buhari Cewa an kamasu? Kada kayi saurin fushi."
- Aminu Garba Isa
“Kaji wani Shirme Buhari Yasa ko kuma Shi ya turo su ? Ko kuma Kai Kasan da Sanya Hannun Buhari Suka kama 'Yan uwanka ? Wannan Soki Burutsune kawai irin Naka Wallahi.
- Badamasi Rijiyar Lemu
"Malam sarajo saidu sokoto muna tare kwankwasiyya Alharin ta ga yan Nigeria."
- Abubakar Ibrahim
Asali: Legit.ng