Buhari bai ci amanar Tinubu a zabe ba – Jigon APC ya bayyana asalin abin da ya faru a 2015

Buhari bai ci amanar Tinubu a zabe ba – Jigon APC ya bayyana asalin abin da ya faru a 2015

  • Osita Okechukwu ya bayyana cewa Muhammadu Buhari bai ci amanar Bola Tinubu a zaben 2015 ba
  • Darekta Janar na VON ya maida martani ga Bisi Akande wanda yace Buhari ya saba alkawarin da ya yi
  • Okechukwu yace dama can ba ayi cewa za a ba Tinubu kujerar mataimakin shugaban kasa a 2015 ba

Abuja - Darekta Janar na VON, Osita Okechukwu yace babu wata yarjejeniya da aka yi tsakanin Muhammadu Buhari da Asiwaju Bola Tinubu a zaben 2015.

A ranar Litinin, 20 ga watan Disamba, 2021, jaridar Punch ta rahoto Mista Osita Okechukwu yana musanya abin da Cif Bisi Akande ya rubuta a cikin littafinsa.

Osita Okechukwu yace shugaban kasa Muhammadu Buhari bai yi alkawarin zai ba Bola Tinubu kujerar mataimakin shugaban kasa da za ayi takarar 2015 ba.

Kara karanta wannan

Takarar 2023 na neman raba kan Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo da Ubangidansa Tinubu

Okechukwu wanda da su aka kafa jam’iyyar APC ya bayyana wannan ne a jiya a lokacin da yake zantawa da manema labarai a wajen wani biki a birnin Abuja.

‘Dan siyasar ya yi bayanin asalin abin da ya faru a lokacin da za ayi zaben 2015, yace sam bai san da wani alkawari tsakanin Buhari da Asiwaju Bola Tinubu ba.

Buhari da su Tinubu
Akande, Tinubu da Buhari Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Jaridar Newswire ta rahoto Okechukwu yana mai cewa Tinubu ya taimaka wajen nasarar 2015.

Abin da ya sa Tinubu bai zama mataimakin Buhari ba

“Ina cikin ‘yan Buhariyya da ke matukar ganin girman Asiwaju (Bola Tinubu) saboda yadda ya ba zaben Buhari karin goyon baya a takarar 2015.”
“Dama can Buhari ya na da kuri’u miliyan 12, amma bai iya yin nasara a zabukan 2003, 2007, 2011 ba, sai da ya hada-kai da sauran jam’iyyu.”

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban kasa ta jero tulin nasarorin Shugaba Buhari yayin da ya cika shekara 79

“Abin da na sani shi ne an yi ta kai-komo a kan maganar tsaida musulmi da musulmi, ko akwai tabbacin zai ba APC nasara a zaben shugaban kasa.”
“Abin da na sani shi ne wannan ne ya jawowa Tinubu cikas a wajen samun kujerar mataimakin shugaban kasa, ba wata yarjejeniya aka saba ba.”
“An duba abin da ya faru a zaben 1993 na Abiola/Kingibe, aka ga ba zai yiwu yanzu ba.” – Chidoka.

Ana harin kujerar shugaban kasa

Magoya bayan Farfesa Osinbajo da Bola Tinubu sun dage da kamfe, suna harin kujerar Muhammadu Buhari duk da ba a fara shirin zaben 2023 ba.

An ji Osita Okechukwu ya na cewa abin da ya kamata shi ne tsohon gwamnan Legas, Tinubu ya janye batun takara, ya bi bayan wani matashi mai jini a jika.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng