2023: Kada ku sake kuskuren amincewa da jam'iyyar PDP, Shugaban Majalisa ga yan Najeriya

2023: Kada ku sake kuskuren amincewa da jam'iyyar PDP, Shugaban Majalisa ga yan Najeriya

  • Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, yace jam'iyyar PDP ba ta taɓuka komai ba na tsawon shekara 16 tana mulki
  • Yace shugaba Buhari ba ya iya rintsawa ko na dakika ɗaya a kokarinsa na kawo cigaban ƙasa ga yan Najeriya
  • A cewar shugaban Sanatocin gwamnan Gombe ya cancanci ya zarce zango na biyu a kujerararsa

Gombe - Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya roki matasan jihar Gombe da na ƙasa baki ɗaya kada su sake kuskuren amincewa da PDP.

Lawan ya yi wannan furuci ne ranar Lahadi a wurin taron shirin koyar da sana'o'i da sanatan Gombe ta arewa ya shirya, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Shugaban babbar majalisar ƙasa ya bayyana cewa tsawon shekaru 16 da PDP ta kwashe kan madafun iko, babu wani tsayayyen aikin cigaba da ta kawo wa ƙasa.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 4 da kasurgumin dan bindiga, Bello Turji, ya nema a wasikar sulhu

Sanata Ahmad Lawan
2023: Kada ku sake kuskuren amincewa da jam'iyyar PDP, Shugaban Majalisa ga yan Najeriya Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

A cewar sanatan, zai zama babban abin dana sani da kuma takaici ga matasan Najeriya ace PDP ke jagorantar su.

Vanguard ta rahoto Lawan yace:

"Ba abin da PDP ta tsinana tsawon shekara 16, sun kashe dukiyar ƙasa ba tare da yin wani aikin cigaba ba. Bai kamata matasa su sake yarda da jam'iyyar PDP ba."

Buhari ba ya hutawa don cigaban Najeriya - Lawan

Shugaban sanatocin ya ƙara da cewa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya nuna kwarewa da salon mulki kuma ya gwangwaje yan Najeriya da romon demokaradiyya.

Sanata Lawan ya bayyana cewa shugaba Buhari bai taɓa hutawa na dakika ɗaya ba tun lokacin da ya karɓi ragamar mulkin kasar nan a 2023.

"Muna ƙara gode wa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, shine jagoran jam'iyya na ƙasa, wanda ya shugabance mu tun daga 2015 zuwa yau.

Kara karanta wannan

Zamfara: Kasurgumin dan bindiga, Bello Turji, ya aike da wasikar neman sulhu ga shugaba Buhari, Matawalle

"Shugaban ya nuna bukatar gyara ƙasar nan, shugaban ƙasa bai taba hutawa na dakika ɗaya ba."

Lawan ya nuna goyon baya ga gwamnan Gombe

Sanata Lawan ya goyi bayan tazarcen gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Yahaya, inda yace mutanen Gombe sun ga canji tun daga 2019.

"Mai girma gwamna, a madadin majalisar dattawa da majalisar tarayya, mun yaba wa kokarin ka kuma mun ce 4 + 4."

A wani labarin kuma An maka tsohon gwamna gaban kotu kan ya ƙi neman takarar shugaban ƙasa a 2023

Wasu masu kishin ƙasa sun maka tsohon gwamnan Abia gaban kotu kan ya ƙi fitowa takarar shugaban ƙasa a 2023.

A cewarsu, suna bukatar kotu ta tilasta masa nuna sha'awar neman takara, domin shi kaɗai ya rage da zai iya ceto Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262