Farin jinin Shugaba Buhari ya yi mummunan sauka bayan hare-hare da kashe-kashe a Arewa
- Vanguard for Good Governance Initiative ta gudanar da bincike a kan farin jinin Muhammadu Buhari
- Sakamakon binciken ya nuna karbuwar Muhammadu Buhari ta ragu sosai a karshen shekarar nan ta 2021
- Rashin tsaro da ya addabi jihohin Arewa ya na cikin abubuwan da suka jawowa karbuwar Buhari cikas
Nigeria - Farin jinin shugaba Muhammadu Buhari ya yi kasan da bai taba yi ba tun da ya karbi mulki daga hannun Goodluck Jonathan a Mayun 2015.
Wani bincike da Vanguard for Good Governance Initiative tayi, ya nuna cewa a cikin ‘yan kwanakin nan, karbuwar shugaban kasar ta ragu sosai.
Daily Reality tace al’umma sun fara cire rai da nuna fushinsu ga gwamnatin APC ta Muhammadu Buhari yake jagoranta ne saboda matsalar rashin tsaro.
Jaridar ta fitar da rahoto cewa, yardar da aka yi wa shugaban kasar ya ragu daga 58% zuwa 21%. Farin jinin shugaban kasar ya yi kasa ne a watanni biyu.
Meya faru ake barin jirgin Buhari?
Idan aka bi binciken daki-daki, za a ga cewa matsalar rashin tsaro yana cikin dalilan samun canjin.
Jama’a musamman daga Arewacin Najeriya ba su jin dadin yadda lamarin tsaro ya tabarbare, inda aka sace mutane kusan 400 a watannin bayan nan.
Wata matsala da ake samu da gwamnatin Muhammadu Buhari ita ce yadda ta gaza shawo kan matsalar tattalin arziki, har yanzu mutane su na kokawa.
Matsin lamba, hauhawan farashin kaya da tsadar abinci su na cikin abubuwan da suka jawo mutanen da suka yi amanna da Buhari, suke barin jirginsa.
Tasirin IPOB a Kudu maso gabas
Binciken da Vanguard for Good Governance Initiative ta gudanar ya nuna ta’adin da ‘yan kungiyar IPOB suke yi, ya na nakasa tattalin arzikin kudu maso gabas.
VGGI tace ta gudanar da binciken ne ta hanyar yin waya, aika sakonnin imel, hira da tattaunawa da mutane sama da 150, 000 a watanni uku domin jin ra’ayinsu.
Abubuwa sun fara sauki a Katsina
A yau ne aka ji cewa Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari da wasu dattawan jihar sun hadu da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Aso Rock Villa.
Masari ya yi magana a kan kokarin da suke yi na kawo zaman lafiya a Arewacin Najeriya da kuma wadanda suke je har gida, suka kashe kwamishinansa.
Asali: Legit.ng